You are here: HomeAfricaBBC2023 08 27Article 1832813

BBC Hausa of Sunday, 27 August 2023

Source: BBC

An bai wa Van Dijk jan kati a karon farko a Liverpool

Virgil van Dijk Virgil van Dijk

An bai wa Virgil van Dijk jan kati a ranar Lahadi a gasar Premier League a karawar Liverpool da Newcastle United a St James Park.

A minti na 27 aka kori dan kwallon Netherlands ɗin bayan da ya yi wa Alexander Isak ƙeta. A lokacin an ci Liverpool 1-0 a wasan mako na uku a Premier.

Wannan ne karon farko da aka bai wa Van Dijk jan kati a Liverpool da kuma babbar gasar tamaula ta Ingila.

Kazalika, shi ne karo na biyu a jere da aka kori dan wasan Liverpool a Premier League, tun bayan Maris/Afirilun 2015 a wasa da Man United da kuma Chelsea.

Kafin nan jan kati biyu 'yan kwallon Liverpool suka karɓa a fafatawa 139 a Premier League.

A makon wasan Premier League na biyu a ranar 19 ga watan Agusta, inda Bournemouth ta sha kashi da ci 3-1 har gida a hannun Liverpool, an bai wa Alexis Mac Allister jan kati.

Daga baya hukumar kwallon kafa ta Ingila ta soke katin da aka ba wa Mac Allister, wanda ya samu damar buga wasa da Newcastle ranar Lahadi.

Ranar 1 ga watan Janairun 2018, Liverpool ta ɗauki Van Dijk daga Southamton.

Ya karbi jan kati biyu a Southampton, inda ya buga karawa 231 a Premier League da cin kwallo 20 da bayar da uku aka zira a raga.