You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896683

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

An ajiye Bailly da wasu 'yan wasa hudu saboda rashin kokari a Besiktas

Eric Bailly, tsohon dan wasan Manchester United Eric Bailly, tsohon dan wasan Manchester United

Tsohon dan wasan Manchester United, Eric Bailly yana cikin 'yan wasa biyar da Besiktas ta ajiye su, saboda rashin kokari.

Mai shekara 29 dan wasan tawagar Ivory Coast, ya koma kungiyar ta Turkiyya ne daga Manchester United a watan Satumba.

Sauran 'yan wasan da aka ajiye sun hada da Vincent Aboubakar da Rachid Ghezzal da Jean Onana da kuma Valentin Rosier.

Bailly wanda ya taka leda a Old Trafford tsakanin 2016 zuwa 2023, ya buga wasa takwas a Besiktas.

An fahimci cewar ba a soke kwantiragin 'yan wasan ba, amma an cire su daga jerin wadanda ke buga mata wasanni, kuma ba sa atisaye tare da sauran 'yan kwallon.

Besiktas, wadda Riza Calimbay ke jan ragama, tana mataki na shida a teburi da tazarar maki 14, tsakaninta da 'yan biyun farko wato Fenerbahce da Galatasaray bayan buga wasa 15.

An kuma fitar da kungiyar daga Europa Conference League, wadda ta zo ta karshe, kuma an doke ta wasa biyar a cikin rukuni.

Bailly ya yi kaka biyar a Old Trafford bayan komawa can daga Villarreal a kan £30m a 2016, wanda ya buga mata karawa 113.

Kyaftin din Kamaru, Vincent Aboubakar, mai shekara 31 da takwaransa, Onana mai shekara 23 sun koma Besiktas a kakar nan.

Shi kuwa dan kasar Faransa Rosier, mai shekara 27 da dan Aljeriya, Ghezzal, suna kungiyar tun 2020.