You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816565

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Amurka ta tsallaka zagayen gaba da kyar a gasar Kofin Duniya

Hoton alama Hoton alama

Tawagar Amurka mai rike da kofin gasar Kofin Duniya ta mata ta sha da kyar a hannun Portugal inda ta tsallaka zagayen 'yan 16 a gasar da ake bugawa a Australiya da New Zealand.

Wannan ne karon farko da matan Portugal ɗin suka halarci gasar.

Amurka ba ta taka wata rawar gani ba a gasar, inda ta yi canjaras a wasanta na biyu da Netherlands, yanzu kuma ta sake yin kunnen doki da Portugal.

A karshe dai Amurka ta yi farin cikin jin cewa sakamakon ya isa ya taimaka mata wurin ketarawa zagaye na gaba a matsayi na biyu a rukunnin bayan Netherlands ta lallasa Vietnam 7-0.

Yanzu dai Amurka, wadda ita ce ke matsayi na daya a duniya wajen taka leda, za ta kara da wadda ta ja ragamar rukunin G, wanda za a tantance ranar Laraba.