You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809527

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Amurka ta tabbatar Ukraine na amfani da bam mai 'ya'yan da ta bata

Fadar White House Fadar White House

Fadar White House ta tabbatar da cewa Ukraine na amfani da bam ɗin nan mai 'ya'ya da Amurka ta ba ta kan dakarun Rasha da ke ƙasar.

Kakakin ma'aikatar tsaron ƙasar John Kirby ya ce bayanan da suka samu sun tabbatar da cewa Ukraine na amfani da ban ɗin yadda ya kamata, a hare-haren ramuwar da take kai wa dakarun Rasha.

Bam mai 'ya'ya dai na watsuwa ne wurare daban-daban idan aka harba shi, kuma sama da ƙasashe 100 na duniya sun sanya hannu kan yarjejeniyar haramta amfani da shi saboda haɗarinsa ga fararen hula.

Amurka ta amince ta bai wa Ukraine shi, domin ƙara mata ƙarfin gwiwa a yaƙin da take lokacin da ta ce harsashenta sun tasamma ƙarewa.

Ukraine ta yi alƙawarin amfani da wannan bam a iya inda dakarun Rasha da take yaƙi da su suke.

"Suna amfani da su yadda ya kamata," in ji Kirby. "Suna kai hari da su suna samu kuma suna yin abin da ake harba su dan shi. Ina ganin iya nan zan yi bayani."

Amurka ta yanke shawarar aika wa da ban ɗin bayan da Ukraine ta yi koken harsashenta sun ɗauki hanyar ƙarewa lokacin da ta fra kai hare-haren ramuwa, waɗanda suke tafiyar wahainiya sama da yadda aka yi tsammani tun da fari.

Shugaba Joe Biden ya kira wannan mataki "mai wuyar gaske" yayin da ƙawayen ta irinsu Burtaniya da Canada da New Zealand da Spaine suka ƙalubalanci amfani da bam ɗin.

Bam ɗaya ake harbawa cikin makamin atilare sai ya watsu zuwa yankuna masu nisa, kuma zai iya kwahe shekaru kafin ya fashe.

Makamin yana aiki sosai musamman kan dakarun sojin da suke maƙalewa cikin ramuka, tunda fashewa yake ya watsu wurare masu yawa, kuma haɗari ne kai-kawo a irin yankunan har sai an tabbatar da babu barazana.

Rasha na mafani da irin wannan bam tun lokacin da ta fara mamaya a Ukraine a bara, kuma har a yankunan fararen hula.

Da yake mayar da martani kan wannan bam da Amurka ta bai wa Ukraine, Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa na da irin wannan makami "kuma za ta yi amfani da shi da zarar an yi amfani da shi a kanta".

Oleksandr Syrskyi, wani Janar ɗin Ukraine ne da ke lura da yakin da ake yi a gabashin ƙasar, ya shaida wa BBC a makon jiya cewa, dakarunsa na buƙatar wannan bam domin kare kanta daga ɓarnar da maƙiyansu ke yi musu.

"Muna fatan samun sakamako mai kyau cikin gaggawa, amma azahiri abu ne mai wuya. Yawan sojojinsu da suka mutu a nan, yawan tambayar da 'yan uwansu za su riƙa yi a Rasha,"

Ya ƙara da cewa muna buƙatarsa dun da cewa bam mai 'ya'ya ba zai "kawar da matsalarmu ba".

Ya amsa cewa amfani da su cike yake da ruɗani, "amma idan har Rasha ba ta yi amfani da shi ba muma ba za mu yi amfani da shi ba."