You are here: HomeAfricaBBC2023 01 03Article 1689890

BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

Source: BBC

Amurka ta mayar wa Masar akwatin gawa na zamanin Fir'auna

Akwatin gawa da aka sassaka da dutse Akwatin gawa da aka sassaka da dutse

Amurka ta mayar wa dasar wani akwatin gawa da aka sassaka da dutse, wanda Amurkar ta ajiye a gidan kayan tarihinta.

Akwatin mai tsawon mita 2.9 (ko kuma kafa 9.5) tun na zamanin mutanen baya, da masarautar Fir'auna, wanda wani malamin coci da ake kira Ankhenmaat ya mallaka shekara 664 zuwa 332 kafin haihuwar annabi Isa.

An sace akwatin daga makabartar Abu Sir da ke arewacin Masar a 2008, wanda wani kamfanin bibiyar kayayyakin tarihi ya ɗauke kuma ya bi da shi ta cikin Jamus zuwa Amurka.

Wanda aka bai wa akwatin ya karɓe shi ne a matsayin aro kuma ya ajiye shi a gidan tarihi na (Houston Museum of Natural Science ) a 2013.

An mayar da akwatin gawar ne Masar bayan wani bincike da aka shafe shekaru ana yi kuma a hukumance ofihin jakadancin Amurkan ya miƙa shi a wani ɓangare na wani buki da ya gudana a Alƙahira a ranar Litinin.

Ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya halarci taron tare da takwaransa na harkokin yawon buɗe ido da kayan tarihi Ahmed Issa.


"Wannan buki na yau cike yake da ɗimbin tarihi na ƙoƙarin kare kayan tarihi da ake yi tsakanin Amurka da Masar," in ji wakilin Amurka a Masar Daniel Rubinstein.

Mista Isa ya ce dawo da akwatin da aka yi ya nuna ƙoƙarin da Masar ke yi na dawo da kayan tarihinta da aka sace.

A watan Satumban da ya gabata, wani babban jam'i a yankin Manhattan Alvin Bragg ya ce an sace akwatin wanda darajarsa ta wuce dalar Amurka miliyan daya, ba bisa ƙa'ida ba, kuma gungun masu safarar kayan tarihi na duniya ne suka aikata hakan.

Kuma wannan gungun ne ke da alhakin sace wani akwatin gawa da aka sassaka da zinare, wanda a 2019 aka mayar da shi Masar, kuma shi ma an sassaƙa shi ne tun lokacin mutanen da, an bai wa masar shi a 2020 tare da wasu kayan tarihi biyar.

Ba Amurka ba ce kaɗai ta mayar wa Masar kayan tarihin da aka sace a baya-bayan nan ba.

A 2021, Isra'ila ta mayar wa Masar ɗin wasu kayan tarihi 95 da aka sace aka gano su a cikin wata kasuwar birnin Kudus.