You are here: HomeAfricaBBC2023 06 26Article 1793027

BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

Alfarma ce da jin daɗi wasa a Man City - Gundogan

Ilkay Gundogan Ilkay Gundogan

Ilkay Gundogan ya ce "babu wani abu cikin wasa a Man City sai jin daɗi da dama mai yawa".

Ɗan wasan ya shaida haka ne bayan komawarsa Barcelona lokacin da kwantaraginsa ta ƙare da ƙungiyar, inda ya bar ta ba tare da eje ba.

Duk da cewa City ta yi masa tayin ƙarin kwantaragi amma Gundogan ya dage shi sai ya koma ƙungiyar ta Sifaniya a wannan kaka na tsawon shekara biyu, yana kuma da zaɓin tsawaita kwantaragin na ƙarin shekara guda.

Dan wasan mai shekara 32 dama kwantaraginsa za ta ƙare ne a City a watan Yunin bana.

"Manchester ta zama gida a gare ni, kuma ina jin cewa nima ina cikin iyalai masu mahimmanci a City," a cewar ɗan wasan tsakiyar Jamus ɗin.

Gundogan ya buga wasanni 51 a kakar 2022/2023 ya kuma ci kwallo 11, kuma yana cikin 'yan wasa masu mahimmanci a kofi uku da City ta ɗauka a bana.

Ya ci kwallo shida a wasanni bakwai na ƙarshe da ya buga - ciki har da kwallo biyu da ya ci a wasan ƙarshe na gasar FA da suka yi nasara kan Manchester United.

Idan Gundogan ya koma Barcelona kwantaragin sayar da shi sai ƙungiyar da ta taya shi yuro miliyan ɗari huɗu.

A 2016 ya koma City daga Borussia Dortmund kan kuɗi fan miliyan 20, kuma shi ne ɗan wasan farko da Pep Guardiola ya saya a ƙungiyar.

A zamansa a ƙungiyar Gundogan ya buga wasanni 304 ya ci kwallo 60 ya kuma ci manyan kofuna 12.

Ya ci gasar Premier biyar ya ci gasar Champions ɗaya ya ci kofin FA biyu sannan kuma ya ci kofin Carabao huɗu.

Ya ce yana da abubuwan tunawa masu yawa a zamansa a City, musamman cin kofuna uku a shekara da ya yi wanda ba zai taɓa mantawa da shi ba.

"Ina son yi wa kocina Pep godiya da ya yarda da ni ya ba ni dama, kazalika abokan taka leda na, sannan magoya bayan masu ban mamaki da ba za a taɓa mantawa da su ba."