You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811957

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Alex Telles ya koma Al-Nassr daga Man United

Alex Telles Alex Telles

Ɗan kwallon tawagar Brazil, mai tsaron baya, Alex Telles ya koma taka leda a Al-Nassr daga Manchester United.

Telles, mai shekara 30, zai taka leda tare da tsohon ɗan wasan United, Cristiano Ronaldo, wanda ya koma buga babbar gasar Saudi Pro League a watan Janairu.

Kungiyoyin biyu ba su fayyace kuɗin cinikin ɗan kwallon Brazil ɗin ba.

Telles ya yi wasa 50 a United tun bayan da ta ɗauko shi daga Porto kan fam miliyan 13.6 a 2020, wanda ya yi wasannin aro a Sevilla a kakar da ta wuce.

A kakar bana, babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia ta ɗauki fitattun 'yan kwallo, ciki har da Karim Benzema, wanda kwantiraginsa ya kare a Real Madrid.

Telles shi ne na baya-bayan nan daga Premier League da ya koma zai buga Saudi Pro League da ya haɗa da N'Golo Kante daga Chelsea da ɗan wasan Liverpool Roberto Firmino.

Telles, wanda ya yi wa Brazil wasa 12 da guda biyu a kofin duniya a Qatar a 2022, ya yi takarar buga gurbin lamba uku tare da Luke Shaw a Old Trafford.