You are here: HomeAfricaBBC2023 08 07Article 1820210

BBC Hausa of Monday, 7 August 2023

Source: BBC

Albarkar shayar da jariri nonon uwa

Dr Mariya Mukhtar Yola Dr Mariya Mukhtar Yola

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce shayar da jarirai nonon uwa, na ɗaya daga cikin hanyoyin ingantattu don tabbatar lafiyar yaro da tsawon kwanansa.

Sai dai saɓanin shawarwarin Hukumar Lafiya ta Duniya, kimanin rabi na jarirai 'yan ƙasa da wata shida ne kawai ake shayar da su da nonon uwa zalla.

Ta ce nonon uwa shi ne abincin da ya dace ga jarirai kuma yana da aminci da tsafta, sannan ya ƙunshi wasu sinadarai da ke kare jarirai daga kamuwa daga cutuka masu yawa.

Amma duk da muhimmancinsa, mata ma'aikata fiye da rabin biliyan ɗaya ne da ke aiki ne ba sa samun kariyar dokokin ƙasa da ta dace ga mata masu jego.

Haka kuma kashi 20 ne kawai na ƙasashen duniya ne ke buƙatar iyayen gida a wuraren aiki ke bai wa ma'aikata hutu da abubuwan da suka dace don shayar da jariransu.

Albarkacin Makon Shayar da Jarirai Nonon Uwa na Duniya, Dr Mariya Mukhtar Yola ta yi mana bayani game da muhimmancin bai wa jariri mama zalla a cikin wata shida na faron rayuwa.