You are here: HomeAfricaBBC2023 11 23Article 1886465

BBC Hausa of Thursday, 23 November 2023

Source: BBC

Al’amurra sun cabe a arewacin Najeriya — Babachir Lawal

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya a Najeriya, Babachir Lawal, ya ce zaben 2023 ya raba kan jama`a, musamman al`umar arewacin kasar, kuma da wuya yankin ya ci gajiyar siyasa idan al`umomin yankin ba su kawar da bambance-bambancen addini da kabilanci da ke tsakaninsu ba.

A hirarsa da BBC Mista Babachir Lawal, ya ce rarrabuwar ta yi kamarin da mafi yawan al`umma sun koma zaman-karofi sakamakon rashin yarda.

"Yanzu al’amura sun cabe a arewa baki daya"

"Yanzu kowa a arewa zaka ji ba abin da ya ke sai korafi, su kansu a'lummar arewar sun rabu kashi biyu wato kirista da musulmi, hatta a tsakanin kiristan ma akwai kablu da dama," in ji tsohon sakataren gwamnatin na Najeriya a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ya kuma ce irin wannan rarrabuwa ita ake gudu.

"Idan har kawunan al’ummar arewa a rabe ya ke ta ina za a samu hadin kai da za a samu ci gaba," in ji shi.

‘‘ A yanzu babu wani a arewacin Najeriya da za a kira taro don a zo a hada kai babu, kodayake akwai kungiyoyin da ke kokarin ganin an samu hadin kan amma har yanzu shiru.“

Babachir Lawal, ya ce,“Mu mun dade muna irin wannan kira a kan azo a hada kai amma ba a saurarenmu, shi ya sa ala tilas muka zama ‘yan kallo.“

Tsohon sakataren gwamnatin na Najeriya, ya ce duk abin da muka ce zai faru gashi nan yana faruwa muna gani.

Ya ce,“ Matsalar ita ce mutane ba sa ganin matsalar da ke damunsu, a don haka ni banga abin da za mu iya yi wa arewa ba don abin da ake gudu ya riga faru, musamman idan aka kalli irin halin da arewa ke ciki a Najeriya.“

Mista Babachir ya yi wadannan kalaman ne tare da yin kira a zo a hada kan arewa.

"Yanzu abin da muke so shi ne idan akwai wadanda suke ganin za su iya kawo gyara a arewa to gara su fara tun da wuri." in ji shi.