You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816604

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Alƙawura biyar da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a jawabinsa

Bola Ahmed Tinubu Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ma'aikatan ƙasar alƙawarin cewa nan gaba kaɗan gwamnatinsa za ta ƙara musu albashi, kamar yadda ya bayyana cikin jawabinsa a yammacin Litinin.

Kazalika ya sake cin alwashin ɓullo da matakan sauƙaƙa wa 'yan ƙasa raɗaɗin da suke ji na cire tallafin man fetur, wanda ya ce "wasu mazambata ne ke amfana da shi".

"A cikin wata biyu, mun adana sama da naira tiriliyan ɗaya na tallafin mai da ake kashewa kan abin da babu riba kuma 'yan sumoga da mazambata ke amfana," kamar yadda ya bayyana.

Sai dai cikin jawabin da shugaban ya gabatar na minti 20 ta kafar talabijin ɗin gwamnatin ƙasar, Tinubu ya nemi 'yan Najeriya su ƙara haƙuri.

Cikin matakan da gwamnatin ta Tinubu ɗauka, akwai ba da umarnin rarraba tan 200,000 na hatsi a faɗin ƙasar don a sayar kan "sassauƙan farashi".

Sai dai jawabin shugaban bai taɓo batun soke tsauraran sharuɗɗa ba game da bashin kuɗin karatu, wanda gwamnatinsa ta ba da sanarwa jim kaɗan kafin ya fara jawabin.

Ga wasu alƙawura biyar da shugaban ya yi wa 'yan ƙasar.

'Za mu ƙara muku albashi'

Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na dab da ƙara wa ma'aikatan Najeriya albashi.

"Ƙarin albashi na nan tafe," a cewarsa. "Da zarar mun daddale game da mafi ƙarancin albashi da kuma sauran abubuwa, za mu saka shi cikin kasafin kuɗi domin fara aiki da shi cikin gaggawa.

"Tuni mun ƙaddamar da tsarin sake duba albashin ma'aikata."

Bai wa kamfanoni 75 rancen biliyan 75

Bugu da ƙari, shugaban ya ce manufarsu ita ce samar da aikin yi ta hanyar bai wa kamfanoni 75 rancen kuɗi naira biliyan 75 cikin wata tara masu zuwa.

"Don ƙarfafa ɓangaren samar da kayayyaki da kuma ayyukan yi, za mu kashe naira biliyan 75 daga Yulin 2023 zuwa Maris na 2024. Tunaninmu shi ne bai wa kamfanoni 75 damar haɓaka tattalin arziki.

"Kowane kamfani daga cikin 75 ɗin zai iya samun rancen biliyan ɗaya kan kashi 9 cikin 100 na kuɗin ruwa duk shekara, inda za su biya cikin shekara biyu a matsayin shiri na dogon lokaci, da kuma wata 12 na fara aiki."

Baya ga waɗannan, Tinubu ya ce za su bai wa masu ƙananan sana'o'i tallafin biliyan 50, inda mutum 1,300 za su amfana a ƙananan hukumomi 774 na faɗin Najeriya.

Raba tan 200,000 na hatsi da taki da iri

Haka nan, Shugaba Tinubu ya ce daga cikin matakan da suka ɗauka na rage raɗaɗin akwai rarraba hatsi ga iyalai da kuma taki ga manoma a faɗin ƙasa.

"Za mu tabbatar da cewa akwai abincin da aka saba ci kuma cikin sauƙi," a cewarsa.

"Wannan dalilin ya sa na ba da umarnin fitar da tan 200,000 na hatsi daga rumubun gwamnati don raba wa iyalai a jihohi 36 har da Abuja a farashi mai rahusa.

"Kuma mun ba da umarnin raba tan 200,000 na taki da iri da sauran kayayyaki ga manoman da ke tallafa wa shirinmu na samar da isasshen abinci."

Samar da motocin bas masu amfani da gas

Yayin da 'yan ƙasa ke ci gaba da kokawa kan tsadar man fetur, Tinubu ya ce ɗaya daga cikin shirinsu shi ne samar da motocin bas masu amfani da makamashin gas (CNG).

"Daga cikin shirinmu, za mu fito da motocin bas a faɗin johohi da ƙananan hukumomi don ɗaukar fasinja a farashi mai sauƙi.

"Mun samar da hanyoyin kashe naira biliyan 100 daga yanzu zuwa watan Maris na 2024 don kawo rukuni 3,000 na motocin da ke amfani da gas (CNG)."

Noma kadada 400,000 ta shinkafa, masara, alkama, rogo

Har wa yau game da noma, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta kashe naira biliyan 200 cikin 500 da majalisa ta amince masa wajen haɓaka noman shinkafa da masara da alkama da rogo.

"Za mu kashe biliyan 50 wajen noma kadada 150,000 ta shinkafa da masara kowannensu.

"Sannan kuma, mu kashe biliyan 50 wajen noma kadada 100,000 ta alkama da rogo kowannensu."