You are here: HomeAfricaBBC2023 11 16Article 1882445

BBC Hausa of Thursday, 16 November 2023

Source: BBC

Al-Shifa: Abin da muka sani game da farmakin da Isra'ila ta kai babban asibitin Gaza

Hoton alama Hoton alama

Sojojin Isra'ila sun kai samame a babban asibitin Gaza, a wani abin da suka bayyana a matsayin wani harin da aka kai wa kungiyar Hamas.

Wani ganau a asibitin Al-Shifa ya shaida wa BBC cewa sojoji sun shiga asibitin cikin dare suna yi wa mutane tambayoyi.

A ranar Laraba, Isra'ila ta ce ta gano "cibiyar aiki" ta Hamas a asibitin, inda ta wallafa hotunan makaman Hamas.

Hamas ta musanta cewa tana gudanar da aiki a cikin babban asibitin, kuma BBC ba za ta iya tabbatar da ikirarin ko wane bangare ba.

Babban jami'in jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce ya firgita da harin da Isra'ila ta kai, yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce "ta damu matuƙa" ga marasa lafiya da ta rasa hanyar sadarwa da su.

BBC tana tuntuɓar ɗan jarida da wani likita a cikin asibitin don jin abin da ke faruwa a can, yayin da kuma rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ita ma take bayar da bayanai.

Abin da waɗanda ke cikin asibitin suka ce?

Khader, wani dan jarida a cikin Al-Shifa, ya shaida wa wakilin BBC, Rushdi Abualouf cewa sojojin Isra'ila sun "karɓe iko" da asibitin kuma babu wani harbi da aka yi.

Ya ce tankokin yaƙi shida da dakaru kusan 100 ne suka shiga harabar asibitin cikin dare. Daga nan ne sojojin Isra'ila suka riƙa shiga ɗaki-ɗaki, suna yi wa ma'aikatan da majinyata tambayoyi.

An bayar da rahoton cewa, rundunar sojin Isra'ila ta buƙaci dukkan maza masu shekara 16 zuwa 40 su bar cikin ginin asibitin zuwa harabar asibitin, amma ban da sassan tiyata da na taimakon gaggawa.

Sojoji sun yi ta harbi a iska domin tilasta wa waɗanda suka rage a cikin asibitin fitowa, inji Khader.

Sai dai Muhammad Zaqout, daraktan asibitocin ma'aikatar lafiya ta Gaza da Hamas ke gudanarwa, ya shaida wa Al Jazeera cewa "babu harsashi ko ɗaya" da aka harba - saboda "babu masu nuna turjiya kuma babu wanda aka tsare" a cikin asibitin.

Isra'ila ta ce ta gano cibiyar gudanar da ayyukan Hamas

A ranar Laraba, rundunar ta IDF ta ce harin ya samo asali ne daga bayanan sirri da kuma kamawar aiki, inda ta yi kira ga "dukkan 'yan ta'addan Hamas" da ke wurin su miƙa wuya

A yayin da sojojin suka shiga harabar asibitin, sun yi artabu da wasu 'yan kungiyar Hamas inda suka kashe su, in ji rundunar ta IDF.

Da yammacin Laraba, rudunar sojin Isra'ila ta ce sojoji sun gano "cibiyar bayar da umarni da ajiye makamai da kayan fasaha na aiki" mallakar Hamas a cikin sashen yin hoton jikin ɗan'adam na MRI.

Ta ce tana ci gaba da gudanar da aiki a harabar asibitin, tare da wallafa hotuna da bidiyo da ke nuna makaman na Hamas ne.

A cikin wani faifan bidiyo na tsawon mintuna bakwai, mai magana da yawun hukumar ta IDF, Jonathan Conricus, ya nuna kyamarorin tsaro da ya ce an rufe su, da kuma makaman da ya ce bindigogi ƙirar AK47 ne da aka boye a bayan na’urar daukar hoton MRI.

Har yanzu BBC ba ta iya tantance faifan bidiyon ko inda yake ba.

Amma idan Isra'ila ba ta da wani karin bayani, aikin da sojoji suka yi a cikin asibitin bai samu manyan makaman yaƙi ba, in ji wakilin BBC a birnin Kudus Orla Guerin.

Hamas ta san Isra'ila za ta shiga asibitin, don haka, da a ce suna da cibiyar gudanar da ayyukansu a asibitin, da sun san yadda za su yi su kauce musu ta babbar hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Gaza.

Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya ruwaito cewa har yanzu sojojin ba su sami wata alama ko daya daga cikin mutane 240 da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su ba a harin da aka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe wasu mutum 1,200.

Mamayar asibitin Al-Shifa ya zo ne jim kadan bayan da Amurka ta fito fili ta goyi bayan ikirarin Isra'ila cewa Hamas na ajiye kayanta a ƙarƙashin babban asibitin.

Sai dai Dr Ahmed Mokhallalati, wani likita a Al-Shifa, ya shaida wa BBC cewa fararen hula ne kawai a asibitin.

Ya ce akwai ramukan karkashin ƙasa a kowane gini a Gaza ciki har da asibitin Al-Shifa.

Asibitoci na samun kariya ta musamman a lokacin yaƙi

A cewar dokar jin kai ta kasashen duniya, asibitoci na da kariya ta musamman a lokacin yaƙi.

Wannan yana nufin cewa masu rikici ba za su iya kai hari a asibitoci ba, ko hana su yin ayyukansu na kiwon lafiya.

Za su iya rasa kariyarsu idan wani da ke cikin rikici ya yi amfani da su don aikata wani "aiki mai cutarwa ga abokan gaba".

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce wannan na iya zama wani abu kamar amfani da asibiti a matsayin sansanin kai hari ko matsuguni na mayaka, ko kuma don kare manufar soji daga farmaki.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta sha gargadin Hamas da cewa "ci gaba da yin amfani da asibitin Al-Shifa a matsayin wurin gudanar da aikin sojoji ya kawar da kariyar da take samu", inda ta yi kira da a kwashe majinyata da sauran mutane daga asibitin kafin kai farmakin.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa kwashe marasa lafiya zai zama tamkar "hukuncin kisa", ganin cewa tsarin kiwon lafiyar yana durkushewa.

Ayyukan jin-ƙai na ƙara taɓarɓarewa

Dr Mokhallalati ya shaida wa BBC a ranar Laraba cewa asibitin ba shi da wuta da iskar oxygen da kuma ruwa. A ranar Talata, an gudanar da aikin tiyata ba tare da maganin kashe zafi ba, yayin da marasa lafiya "suke kururuwa saboda raɗaɗi zafi".

Likitoci sun kasa taimaka wa wani majiyyaci da ya ƙone, lamarin da ya sa ya mutu a gabansu.

Dr Mokhallalati ya ce jarirai bakwaini guda shida sun mutu a kwanakin baya.

"Me ya sa ba za a iya kwashe su ba," in ji shi. "A Afghanistan, sun kwashe mage da karnuka."

Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana samar da kwalaben saka jarirai da abincinsu da kuma magunguna.