You are here: HomeAfricaBBC2022 12 30Article 1687973

BBC Hausa of Friday, 30 December 2022

Source: BBC

Al Nassr na son haɗa Ronaldo da Ramos, mai son Enzo sai ya biya £106m

Sergio Ramos Sergio Ramos

Al Nassr na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun sake haɗa ɗan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, da ɗan wasan bayan Paris St Germain mutumin ƙasar Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 36, a kulob ɗinsu. 

Manchester City na shirin biyan fam miliyan 10.6 a shekara don ɗan gaban AC Milan Rafael Leao, yayin da ƙungiyarsa ta Serie A, ita ma za ta riƙa biyan fam miliyan 6.2 duk shekara ga matashin ɗan shekara 23, wanda mahaifinsa ke tattaunawa da City

Tsohon babban jami'in kulob ɗin Birmingham City Xuandong Ren ya ce Man United da Chelsea duk sun yi yunƙuri ba tare da nasara ba wajen ɗauko ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund na ƙasar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, a 2020, duk da tayin biyan sa albashi mai kauri da suka yi. 

Babban jami'in kulob ɗin Shakhtar Donetsk Sergei Palkin ya ce "suna ci gaba da tattaunawa" da Arsenal kan ɗan wasan gefen Ukraine mai shekara 21 Mykhaylo Mudryk, bayan an ce wa Gunners albarka a tayin fam miliyan 55 da suka yi. 

Shaktar na amfani da kuɗin da aka sayi Antony fam miliyan 86 kafin ya je Manchester United daga Ajax bara, a matsayin mizaninsu cinikinsu. 

Shugaban Benfica Rui Costa ya ce ba za su sayar da ɗan wasan tsakiya da ya lashe Gasar cin Kofin Duniya Enzo Fernandez a kan ƙasa da fam miliyan 106 kamar yadda sharaɗin sakin sa ya tanada ba. ChelseaLiverpool da Manchester United duk suna sha'awar ɗaukar matashin mai shekara 21. 

Benfica sun sa ɗan wasan tsakiyar Argentina mai shekara 19, Maximo Perrone, da ke buga wa kulob ɗin Velez Sarsfield, a matsayin wanda zai maye gurbin Enzo Fernandez idan ya tafi. 

Chelsea sun cimma yarjejeniya da Monaco kan ɗan wasan bayanta Benoit Badiashile, mai shekara 21. 

Kocin Tottenham Antonio Conte na son ɗauko ɗan bayan ƙungiyar Bayer Leverkusen daga ƙasar Ecuador Piero Hincapie, mai shekara 20. 

Newcastle United sun bi sawun Manchester United a rige-rigen ɗauko ɗan wasan bayan Lyon na ƙasar Faransa Malo Gusto, mai shekara 19. 

Ɗan wasan gaban Faransa Olivier Giroud, mai shekara 36, ya amince da ƙara kwanturagi da AC Milan inda yanzu zai ci gaba da zama a kulob ɗin har nan da 2024. 

Ɗan wasan tsakiyar Chelsea na ƙasar Italiya mai shekara 31, Joginho na ba da fifiko ga tsawaita kwanturagi da ƙungiyarsa ta yanzu maimakon tafiya zuwa wani kulob ɗin na daban. 

Chelsea na samun ci gaba a tattaunawar da take yi kan wani sabon kwanturagi da ɗan wasan tsakiya na ƙasar Faransa N'Golo Kante, mai shekara 31. 

An yi wa Fulham tayin ɗan wasan bayan Roma Rick Karsdorp, mai shekara 27, bayan matashin na ƙasar Netherlands ya samu matsala da kocinsa Jose Mourinho.

Chelsea ta yi yunƙurin ɗaukar ɗan wasan gaban Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 23, kafin ya cimma yarjejeniya da Liverpool.