You are here: HomeAfricaBBC2023 11 16Article 1882442

BBC Hausa of Thursday, 16 November 2023

Source: BBC

Al-Ittihad na shirin naɗa Marcelo Gallardo a matsayin kocinta

Marcello Gallardo Marcello Gallardo

An sami rahotannin cewa Karim Benzema da N'Golo Kante za su yi atisaye a ƙarƙashin Marcelo Gallardo a Al-Ittihad bayan ta kasa daidaitawa da Julen Lopetegui.

Gallardo dai zai rattaba hannu kan kwantiragi da ƙungiyar har zuwa watan Yunin 2025. Sai dai kuma akwai zaɓin tsawaita kwantiragin na tsawon shekaru biyu har zuwa watan Yunin 2027.

An kori tsohon kociyan, Nuno Espirito Santo, bayan da aka ce sun sami rashin jituwa da Benzema yayin da suka sha kashi da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Asiya a wasan suka yi da ƙungiyar Al-Quwa Al-Jawiya ta ƙasar Iraki.

Ƙungiyar da ke riƙe da kambun gasar ta shirya tsaf domin neman tsohon kocin Sifaniya da Real Madrid, Julen Lopetegui, domin ya maye gurbin ɗan ƙasar Portugal ɗin amma ya ƙi amincewa da tayin saboda yana son komawa gasar Premier.

Wasan farko na Gallardo a matsayin kocin Al-Ittihad zai kasance da ƙungiyar Steven Gerrard Al-Ettifaq a ranar 24 ga Nuwamba a filin wasa na Abdullah Al Dabil a gasar Saudi Pro League.

Al Ittihad ta sami kanta a matsayi na biyar a gasar, inda Al-Hilal ta tesere mata da maki 10 bayan wasanni 13.