You are here: HomeAfricaBBC2023 04 19Article 1752224

BBC Hausa of Wednesday, 19 April 2023

Source: BBC

Akwai jan aiki a gaban Benfica a wasa da Inter a Champions

Romelu Lukaku Romelu Lukaku

Benfica ta je Inter Milan buga wasa na biyu a quarter finals a Champions League, bayan da aka doke ta 2-0 a makon jita.

Ranar 11 ga watan Afirilu, Inter ta doke Benfica 2-0 a wasan farko a Portugal, Nicolo Barella ya fara cin kwallo, sannan Romelu Lukaku ya ci na biyu a fenariti.

Daga wasa tara da aka ci Benfica kwallo biyu ko fiye da hakan a wasan farko sau daya ne kungiyar Portugal ta kai zagayen gaba.

Shine wanda Nurnberg tta ci 3-1 a wasan farko, Benfica ta sharara 6-0 a fafatawa ta biyu a kakar 1961-62.

To sai dai ba a doke Benfica a wasa bakwai baya ba da ta buga a waje, idan ka cire wanda ta yi a cikin rukuni a bana a Champions League.

A karawa hudu da suka yi a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, Inter ta yi nasara a wasa uku da canjaras daya - kenan akwai jan aiki a gaban Benfica kenan.

Wadanda za su iya buga wasan:

Inter: Onana; Darmian, Acerbi, Bastoni; Dumfries, Barella, Hakan Çalhanoğlu, Mkhitaryan, Dimarco; Džeko, Martínez

Wadanda ba za su buga wasan gaba idan aka yi musu katin gargadi: Bastoni, Dimarco, Džeko, Martínez

Benfica: Vlachodimos; Gilberto, António Silva, Otamendi, Grimaldo; Florentino, Chiquinho; Aursnes, Rafa Silva, João Mário; Gonçalo Ramos

Wadanda ba za su buga wasan gaba idan aka yi musu katin gargadi: Gonçalo Ramos, Florentino, João Mário

Wasa tsakanin Benfica da Inter Milan:

Champions League Talata 11 ga watan Afirilu

  • Benfica 0 - 2 Inter


  • UEFA Cup Alhamis 26 ga watan Maris 2004

  • Inter 4 - 3 Benfica


  • UEFA Cup Alhamis 11 ga watan Maris 2004

  • Benfica 0 - 0 Inter


  • European Cup Alhamis 27 ga watan Mayu 1965

  • Inter 1 - 0 Benfica


  • Tun bayan da Benfica ta kai wasan karshe a European Cup a 1990, an fitar da kungiyar ta Portugal a quarter finals karo biyar a Champions League.

    Wannan shine wasan farko da Inter ta kai quarter finals tun bayan shekara 12, tun daga nan ba ta kara abin kirki ba, bayan lashe kofin a 2010.