You are here: HomeAfricaBBC2021 05 01Article 1248481

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Adeyemi da Remi Tinubu: Matar Bola Tinubu ta soki Sanatan da ya ce babu tsaro a Najeriya

Hotun Remi Tinubu da Smart Adeyemi Hotun Remi Tinubu da Smart Adeyemi

Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya sun yi musayar zafafan kalamai sakamakon rashin tsaron da ke ci gaba da ta'azzara a kasar.

Sanatocin, Smart Adeyemi daga jihar Kogi da Remi Tinubu daga jihar Lagos, suna cikin wadanda suka bayar da gudunmawa yayin muhawarar da majalisar dattawan ta gudanar ranar Talata.

Majalisar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zage damtse domin magance rashin tsaron da kasar ke ci gaba da fama da ita.

Sai dai kalaman da Sanata Smart Adeyemi ya yi cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa domin magance matsalar sun fusata takwararsa Sanata Remi Tinubu.

Dukkanin Sanatocin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin kasar ce.

Sanata Adeyemi ya ce: "Wannan ita ce matsalar tsaro mafi muni da muke fuskanta. A hakikanin gaskiya, wannan matsalar ta fi ta Yakin Basasa muni," in ji shi.

Ya kara da cewa "bai kamata mu rika siyasantar da wannan matsala ta tsaro ba. Babu wanda yake iya yin bacci da ido biyu a kasar nan — daga kudu zuwa arewa. Ba zan iya zuwa Kaduna ba inda aka haife ni saboda rashin tsaro."

A cewarsa, dole Shugaba Buhari ya nuna cewa shi ne shugaban kasar ta hanyar yin gaggawar magance wannan matsala.

Sai dai da alama wadannan kalamai ba su yi wa Sanata Remi Tinubu, matar jigon jam'iyyar APC Bola Tinubu, dadi ba.

Da take yin raddi a gare shi, ta ce Sanata Samart Adeyemi kura ne da fatar akuya.

Ta tambaye shi cewa: "Shin kai dan jam'iyyar PDP (Peoples Democratic Party) ne? Ko kai kura ce da fatar akuya?"

Ta ce a matsayinsa na dan jam'iyyar APC bai kamata ya rika irin wadannan kalamai ba.

Me 'yan Twitter suke cewa?

Wannan batu dai shi aka fi tattaunawa a kansa a shafin Twitter na Najeriya a ranar Laraba, inda 'Remi Tinubu' da 'Smart Adeyemi' suka kasance sunayen da ake amfani da su domin yin tsokaci kan batun.

Da yake tsokaci kan batun, FS Yusuf, ya bayyana cewa bai kamata a rika siyasantar da batun rashin tsaro ba, yana mai cewa "gaba-gadin da Remi Tinubu ta yi wajen gaya wa 'yan Najeirya cewa kasar ka iya konewa idan jam'iyyarsu maras alkibla za ta ci gaba da mulki, wani keta ne da rashin hankali."

Ita kuwa Nefertiti ta yaba wa Sanata Smart Adeyemi wanda ta bayyana a matsayin wayayyen mutum wanda babu ruwansa da batun jam'iyya.