You are here: HomeAfricaBBC2023 01 03Article 1689854

BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

Source: BBC

Abubuwan da za su iya sauya makomar Najeriya a 2023

Hoton alama Hoton alama

Wasa-wasa har an shiga shekarar 2023, kuma a duk lokacin da aka shiga sabuwar shekara, babban fatan da jama'a ke yi a duniya baki ɗaya shi ne samun ci gaba da alkhairai masu ɗorewa a cikin shekarar.

Haka zalika a duk shekara, akan yi hasashen wasu abubuwa da ake sa ran za su iya faruwa sakamakon wasu hujjoji ko kuma abubuwan da ke da akwai a ƙasa da za su iya tabbatar da lamuran.

A Najeriya akwai irin waɗannan abubuwan da tun a bara ake hasashen za su faru a 2023 ganin cewa an riga an yi alƙawarin aiwatar da abubuwan ko kuma lokacin aiwatar da su ya zo.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ake sa ran za su iya faruwa a Najeriya a 2023:

Babban zaɓen 2023

Shekarar 2023 a Najeriya shekara ce mai muhimmanci sakamakon shekara ce da ake sa ran gudanar da zaɓe a karo na bakwai tun daga 1999 bayan komawar ƙasar kan mulkin dimokradiyya.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne ake sa ran gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya, sai kuma a ranar 11 ga watan Maris a gudanar da zaɓen gwamnoni da kuma na ƴan majalisar jihohi.

Cikin waɗanda ke kan gaba a babban zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya akwai Bola Ahmed Tinubu na Jam'iyyar APC da Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP.

Sa'annan akwai Rabiu Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP da kuma Peter Obi na Jam'iyyar LP.

Duk wanda ya yi nasara a cikin ƴan takarar shugabancin ƙasar za a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Sauya ministoci da manyan jami'an gwamnati

Bayan rantsar da sabon shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu, babban abin da za a mayar da hankali a kai shi ne sabbin ministoci da sabon shugaban ƙasa zai naɗa da kuma sabbin shugabannin wasu hukumomin gwamnati da kuma hadiman shugaban ƙasa.

Ministoci dai da hadiman gwamnati na da matuƙar tasiri wurin gudanar da gwamnati da kuma makomar Najeriya ta fuskar ayyukan da gwamnati za ta yi wa al'umma.

Ƙidayar jama'a

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ake sa ran za a yi a 2023 a Najeriya shi ne batun ƙidayar jama'a.

Ana sa ran za a gudanar da ƙidayar jama'ar ne a watan Afrilu, bayan an kammala babban zaɓen Najeriya a watan Fabrairu da Maris.

Ƙidayar da za a yi a Najeriya a 2023 za ta kasance ƙidaya ta biyar da aka yi a ƙasar tun bayan samun ƴancin kan ƙasar a 1960.

Rabon da a yi ƙidaya a ƙasar tun a 2006 da aka yi lokacin mulkin Olusegun Obasanjo inda aka samu adadin mutum miliyan 140.

Ƙidaya dai na da matuƙar amfani domin gwamnati na amfani da ƙididdigar da ake samu wurin shirya wa jama'a ayyuka.

Daina amfani da tsoffin kuɗi da sabbin ƙa'idojin karɓar kuɗaɗe a banki

Wani abu da ake ganin zai iya kawo sauyi ga makomar Najeriya a 2023 shi ne batun daina amfani da tsoffin kuɗi a Najeriya inda ake sa ran daga 31 ga watan Janairu za a daina karɓar kuɗaɗen.

Sai dai duk da an saki waɗannan kuɗaɗe tun a watan Disamba, amma har yanzu jama'a na ta ƙorafi kan cewa kuɗin ba su yawo a hannun jama'a.

Sa'annan kuma a 2023 ake sa ran sabbin ƙa'idojin da babban bankin Najeriya ya fitar za su fara aiki game da cire kuɗi a banki.

Tun da farko CBN ya ce ɗaiɗaikun mutane za su iya cire naira 100,000 ne su kuma kamfanoni za su cire naira 500,000 ne kawai a duk mako.

Sai dai daga baya ya yi amai ya lashe inda ya ce a yanzu ɗaiɗaikun mutane za su iya cire kudi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.

Cire tallafin man fetur

Wani abu da ake fargabar zai shafi ƴan Najeriya kai tsaye a 2023 shi ne batun cire tallafin man fetur.

Tun a shekarar 2022 da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta soma nuna alamun cire tallafin fetur, amma dai ba ta fito ƙiriƙiri ta nuna cewa za ta cire shi ba.

Sai dai duka manyan ƴan takarar shugabancin Najeriya Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu sun bayyana cewa idan sun samu nasarar zama shugaban ƙasa a Najeriya za su cire tallafin fetur.

Babbar fargabar cire tallafin man fetur da ƴan Najeriya ke yi ita ce batun tsadar rayuwa da za ta ƙaru a ƙasar