You are here: HomeAfricaBBC2023 07 03Article 1796702

BBC Hausa of Monday, 3 July 2023

Source: BBC

Abubuwan da suka kamata ku sani game da gasar Wimbledon da za a fara yau

Wimbledon ita ce gasa mafi daɗewa a duniya kuma mafi shahara Wimbledon ita ce gasa mafi daɗewa a duniya kuma mafi shahara

Gasar zakaru kwallon tennis ta Wimbledon kamar yadda ake kiranta, ita ce gasa mafi daɗewa a duniya kuma mafi shahara, game da wannan ko shakka babu.

An fara gasar ne a shekara 1877 wadda hukumar All England Lawn Tennis da Croquet Club ke karɓar baƙuncinta a Wimbledon a London, wadda za a fara a yau.

Cikin jerin manyan gasannin tennis huɗu da ake kira Grand Slams, Wimbledon ce kawai ake bugawa a kan ciyawa, inda daga nan ne aka samo sunan nata na lawn tennis.

Sauran gasa ukun da ake yi, sun haɗa da French Open wadda ake yi kan taɓo, sai Astralian Open da US Open da dukkansu ake yi a kan wani soso mai tauri.

Tun daga zagaye na farko har na ƙarhse na gasar ana fafatawa ne a mataki bakwai, wannan ya haɗa da gasar maza mai ɗan wasa ɗaya da kuma ta mata mai 'yar wasa guda.

Zagayen farko 'yan wasa 128 ne za su fafata a matakin ɗai-ɗaiku.

Zagaye na biyu 'yan wasa 64 ne za su fafata a matakin ɗai-ɗaiku.

Zagaye na uku 'yan wasa 32 ne za su fafata a matakin ɗai-ɗaiku.

Zagaye na huɗu 'yan wasa 16 ne za su fafata a matakin ɗai-ɗaiku.

Zagaye na biyar 'yan wasa takwas ne za su fafata a matakin ɗai-ɗaiku.

Zagaye na shida 'yan wasa huɗu ne za su fafata a matakin ɗai-ɗaiku.

Ko shakka babu mutum biyu ne za su isa matakin wasan ƙarshe na gasar.

Matukar mutum na son lashe gasar mai farin jini sai ya yi nasara a wasa shida da na bwakai kuma sai ya lashe ta.

Kuɗin da za a lashe a gasar baki ɗaya a wannan shekarar ya ƙaru zuwa fan miliyan 44,700,000 an samu ƙarin kashin 10.78 cikin 100 idan aka kwatanta da fan miliyan 40 da aka sanya a gasar a 2022.

Amma idan ana maganar abin da gwarzo ko gwarzuwar gasar za su lashe, zai kai fan miliyan 2,350,000 ƙarin kashi 17.50 idan aka kwatanta da abin da Novak Djokovic da Elena Rybakina suka lashe wata 12 baya.

Bayan haka duk ɗan wasan da ya halarci gasar zai samu kuɗi na ladan zuwansa, domin samun kwarin gwiwar ci gaba da atisaye da kuma kula da kansa.