You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837706

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Abubuwan da suka faru bayan wasan mako na huɗu a Premier

Hoton alama Hoton alama

An kammala wasannin mako na huɗu a Gasar Premier League ta bana a ƙarshen mako, yayin da za a tafi hutu ya zuwa makon gobe don ci gaba da fafatawa.

Mohammed Abdu ya haɗa rahoto a kan ƙwazon da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Firimiya suka yi, kawo yanzu.

Za a buga wasannin shiga gasar nahiyar Turai da ta shiga gasar cin kofin duniya da ta shiga nahiyar Afirka da kuma wasannin sada zumunci.

Bari mu leka don ganin yadda ƙungiyoyin suka taka rawar gani a Premier cikin makon da ya wuce:

Manchester City - Ƙungiyar Etihad da ke kan gaba a saman tebur, ta ci wasa huɗu da ƙwallo 11, amma an zura mata ƙwallo biyu a raga.

Tuni kuma Erling Haaland ya ci ƙwallo shida a wasa huɗun.

Tottenham - Har yanzu ba a lura da wani nakasu a ƙungiyar ba, duk da sayar da Harry Kane ga Bayern Munich a bana.

Sabon koci, Ange Postecoglou ya ƙara saita ƙungiyar tun bayan ɗauko James Maddison, kuma har yanzu ba a ci ƙungiyar ba, sannan tana zura ƙwallaye da yawa a wasa. Amma ta yi canjaras ɗaya, ta ci wasa uku.

Liverpool - Ta yi sauye-sauye da yawa a ƙarƙashin Jurgen Kloop.

Darwin Nunez yana ƙara nuna gogewa, ga kuma ƙwazon Mohamed Salah ko da yake, sashen bayan Liverpool na ɗan yoyo, amma ƙungiyar ta shirya tunkarar kakar bana.

West Ham - Ba Declan Rice? amma ba matasala a ƙungiyar. Wata ƙungiya da a kakar nan, ta nuna za a yi ƙalubalen lashe Premier League da ita.

Mai riƙe da Europa Conference League, za ta buga Europa League a bana.

Ƙungiyar ta doke Chelsea da Brighton, sannan ta ci Luton Town ranar Juma'a.

Arsenal - Doke Manchester United da Gunners ta yi, zai ƙara mata ƙwarin gwiwa, bayan kasa taka rawa mai kyau a karawarta da Crystal Palace da kuma Fulham.

Ya kamata Gunners ta ɗora kwazo daga wannan nasarar da ta yi a kan United a fatan da take da shi na lashe Premier a bana, wadda rabonta da kofin shekara 20 kenan.

Brighton - Idan ka cire wasan da West Ham ta doke Brighton, koci, Roberto de Zerbi na taka rawar gani, inda ya ci ƙwallo 11 a wasa uku, kuma karawar da matashin ɗan wasa Ferguson ya ci Newcastle ƙwallo uku rigis, ta ƙara ƙarfin ƙungiyar.

Nottingham Forest - Maki shida da fara kakar bana, bayan rashin nasara a hannun Arsenal da kuma Manchester United, wadda ta je ta ci Chelsea a Stamford Bridge.

Nasara a kan Chelsea zai ƙara ƙwazon ƙungiyar, wadda ke ganin za ta iya cin kowa a kakar nan, bayan a bara ta yi fama da kaka-ni-ka-yi.

Brentford - Har yanzu ba a doke ta ba, amma ba ta ji daɗin canjaras da Bournemouth da kuma Palace ba. Ƙwallo takwas ta ci kawo yanzu da Bryan

Mbeumo mai huɗu a raga, sun kuma nuna za su kai labari duk da babu Ivan Toney.

Crystal Palace - Wata ƙungiyar da ta fara kakar bana da ƙafar dama kenan, Arsenal ce kaɗai ta doke ta, kuma tana taka leda mai kyau a kakar nan.

Ana tsammanin lallai za a yi tata-ɓurza da ita bana.

Aston Villa - Wadda ta yi ta bakwai a bara, ta doke Everton da Burnley, yayin da ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da kuma Liverpool, kenan tana da maki shida daga wasa huɗun da ta yi.

Fulham - Rasa Aleksandar Mitrovic ya shafi ƙwazon ƙungiyar a kakar nan, wanda shi ne ke ci mata ƙwallaye.

2-2 da ta buga da Arsenal, abin ƙarfafa gwiwa ne, amma sai ta gamu da gagarumin koma-baya a hannun Brentford wadda ta doke ta 3-0.

Wolverhampton - Bayan da ƙungiyar ta canza koci, har yanzu abubuwa ba su hau kan turba ba a kakar nan.

Ko da yake ta doke Everton, wadda ba ta da ƙarfi a bana ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da kuma Brighton.

Sheffield United - Ɗaya daga cikin sabbin ƙungiyoyin da suka hayo Premier League bana, ta samu maki ɗaya tal, amma ta yi ƙoƙari a wasa da City mai riƙe da Premier.

Luton - Wadda ta dawo buga Premier League a kakar nan, bayan shekara 31 - ba ta nuna cewar ta shirya fuskantar ƙalubalen babbar gasar tamaula ta bana ba.

Amma dai tana cikin waɗanda ake ganin da ƙyar ta kai bantenta.

Manchester United - Ta kashe sama da fam miliyan 180 wajen sayo 'yan wasa a bana, amma duk da haka a wasa huɗu ta ci biyu an doke ta karawa biyu, su ne wasannin da Tottenham da Arsenal suka yi nasara.

Ita kuma, ta ci Wolves da Nottingham Forest.

Wasa ɗaya ne a cikin huɗu ta ci ƙwallo fiye da ɗaya - hakan zai nuna maka inda matsalar take - wataƙila dai sabon ɗan wasanta Rasmus Hojland ya share mata hawaye.

Bournemouth - Bayan maye Gary O'Neil, wanda ya hana ƙungiyar faɗuwa a Premier League bara - har yanzu sabon koci, Andoni Iraola yana da jan aiki a gabansa.

Amma dai ƙungiyar ta nuna tana cikin na ƙasan teburi.

Chelsea - Bayan kashe fam biliyan ɗaya a shekara ɗaya da ƙungiyar ta yi, har yanzu ba ta kamo bakin zaren ba ƙarƙashin sabon koci, Mauricio Pochettino.

Wadda ta ci Luton 3-0, an sa ran za ta taka rawar gani a kakar nan, amma West Ham ta doke ta, sannan Nottingham ta yi nasara kanta har gida a Stamford Bridge -- hakan na nufin da sauran gyara a ƙungiyar Stamford Bridge..

Newcastle - An sa buri a kan ƙungiyar, wadda ta yi ta huɗu a bara, ta fara da doke Crystal Palace, amma ta yi rashin nasara a gidan Manchester City.

Sannan Liverpool ta doke ta 2-1 a St James Park, kuma ta yi rashin nasara 3-1 a gidan Brighton.

Kenan wasa uku a jere ta yi rashin nasara, yayin da take shirin buga Champions League a bana.

Burnley - Bayan ta lashe kofin Championship da samun gurbin buga Premier League, an sa ran Vincent Kompany zai nuna kansa a gasar.

Sai dai, ƙwallo 11 aka zura wa ƙungiyar a karawa uku da kuma caskara ta da Tottenham ta yi har gida a wasan mako na huɗu.

Everton - Da ma an yi hasashen cewar ƙungiyar ba za ta taka rawar gani ba a bana, bayan dokar da aka hana ta sayen sabbin 'yan wasa, lokacin da aka same ta da karya ƙa'idar cefanen 'yan ƙwallo.

An sa ran ƙungiyar za ta riƙa cin ƙwallaye bayan ɗaukar Beto da ta yi a kakar nan, amma gwiwa ta yi sanyi sa'ar da Fulham da Wolves da suka doke ta, tun daga nan kuma ake ganin ƙungiyar za ta iya ban kwana da wasannin bana.