You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814153

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

Abu shida da Shugaba Tinubu ya cimma a kwana 60

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu a yanzu ya yi kwana 60 a kan gadon mulki.

Lokacinsa a ofis, ko da yake taƙaitacce ne, amma kuma cike yake da abin da za a iya cewa ɗumbin al'amura, da yawa cikinsu sun ja hankalin jaridu, duk da yake wasu ba domin dalilai na daidai ba.

Har yanzu dai, 'yan adawa suna ƙalubalantar nasarar zaɓensa a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, cikinsu har da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour. Ga alama, duk da haka Tinubu ya zo da shirinsa.

Tafiya ce mai ƙayatarwa ya zuwa yanzu, amma fa ya danganta da waɗanda aka yi magana da su. Tana iya zama mai cike da alhairai, ga wasu kuma sharri.

Mun yi ƙoƙarin kasafta muku yadda tafiyar kwana 60 ta kasance zuwa yanzu a cikin matakai shida.

Tallafin man fetur

Shugaba Tinubu ya sanya mutane zance da karkata kai tashin farko bayan kama ragamar mulkinsa. A ranar da aka rantsar da shi, 29 ga watan Mayun 2023 ya sanar da cewa “Tallafin man fetur ya tafi!”

Wannan sanarwa ta haifar da ruɗani.

Nan take, sai aka fuskanci ƙarancin man fetur. 'Yan kasuwa da dillalai suka ja baki suka yi shiru. Ba da daɗewa ba kuma farashin man fetur a faɗin Najeriya ya yi tashin gwauron zabi daga kimanin N184 zuwa kimanin N488.

Wannan na da ɗumbin tasiri ga halin tsadar rayuwar da ake ciki.

Ko da yake, sanarwar Tinubu ɗorawa kawai ta yi a kan matakan magabacinsa, Muhammadu Buhari, bayan gwamnatinsa ta ce za a dakatar da biyan tallafin mai a ƙarshen watan Yunin 2023, da yawa sun dubi sanarwar tasa a matsayin turin ƙarshe da ya kawo rugujewar tallafin.

Don rage raɗaɗin wahalhalun da cire tallafin man fetur ya haddasa, shugaban ya nemi majalisar dokoki ta amince da karɓo bashin dala miliyan 800.

Tinubu ya ce za a ba da N8,000 ga gida miliyan 12 duk wata daga bashin da za a karɓo daga Bankin Duniya.

Sai dai hakan ya janyo sukar lamiri daga ɓangarori da dama kuma daga bisani Shugaba Tinubu ya ba da umarni cikin gaggawa a sake nazari kan tallafin N8,000 da aka yi niyyar bai wa 'yan Najeriya.

Sauran sauye-sauyen tattalin arziƙi

Tinubu nan take kusan ya shiga aiki, inda ya sanar da wasu sauye-sauyen tattalin arziƙi masu yawa.

Ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Emefiele ne ya ɓullo da shirin canza fasalin takardun naira da kuma ƙayyade kuɗin da mutum zai iya fitarwa a ƙarshen 2022, lamarin da ya haifar da ƙarancin kuɗi da ɗumbin wahalhalu a kan 'yan Najeriya, ana shirin gudanar da manyan zaɓukan 2023.

Shugaba Tinubu ya kuma sanar da matakin dunƙule kasuwannin canjin kuɗi, inda ya maye gurbin tsarin canjin kuɗin ƙasashen waje masu yawa da Babban Bankin Najeriya yake aiwatarwa.

Farashin naira a yanzu ya dogara ne kan yadda kasuwa ta kaya, bisa dunƙulallen tsarin canjin kuɗin, inda Babban Banki kawai yake shiga don tabbatar da daidaituwar harkoki.

Tinubu ya kuma sa hannu kan umarnin shugaban ƙasa huɗu, inda ya ɗage fara biyan haraji a kan harkokin sadarwa da lemukan barasa da dakatar da haraji kan al'amuran gurɓata muhalli ciki har da haraji kan robobin da ke amfani da su sau ɗaya da harajin shigar da wasu nau'o'in ababen hawa cikin ƙasar.

Wannan mataki kamar yadda makusantansa suka ce ya ɓullo da shi ne don magance giɓin da aka gano a cikin manufofin haraji na gwamnatin da ta wuce da kuma taimakawa wajen cimma nasarar manufar sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya.

Kuma yayin da tsadar rayuwa da hauhawar farashin abinci suka ci gaba, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan wadata ƙasa da abinci.

Ya ba da umarnin cewa duk harkokin da suka shafi samar da abinci da ruwan sha da tabbatar da arharsu a matsayin ginshiƙan rayuwa, a shigar da su cikin ikon Majalisar Tsaro ta Ƙasa.

Bashin karatu

Ɗaya daga cikin alƙawurran da Tinubu ya yi shi ne ba za a samu yajin aikin malaman jami'a a lokacin mulkinsa ba.

Wannan ga alama wata manuniya ce da ke tabbatar da irin muradin da yake da shi a ɓangaren ilmi. Babu daɗewa da hawa kan mulkinsa ne, Tinubu ya sa hannu a kan Ƙudurin Dokar Bashin Karatu.

A ƙarƙashin wannan doka, ɗalibai na iya samun bashi don biyan kuɗin makarantarsu.

Sai dai wannan mataki ya gamu da suka daga ɓangarori daban-daban.

Masu sukar lamiri suna tambayar, ta yaya shirin zai yi aiki, idan ma tabbas abin ya iya yiwuwa bisa la'akari da abubuwan da suka faru baya a wasu ƙasashe.

Naɗe-naɗe

Kwana ɗaya kafin cikar wa'adin da tsarin mulkin ƙasar ya shimfiɗa wanda jazaman ne sai shugaban ƙasa ya sanar da ministocinsa, Tinubu ya aika sunayen mutum 28 da yake son naɗa wa ministoci zuwa majalisa.

Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ne ya karanta sunayen ranar Alhamis.

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da shugabar mata a jam'iyyar APC, Betta Edu duk suna cikin jerin sunayen mutanen.

Kafin sannan, shugaban ƙasar ya sanar da naɗe-naɗen muƙamai da dama a gwamnatinsa.

Daga masu ba da shawara na musamman zuwa mataimaka na musamman, cikin ɗoki ana bibiyar nade-naɗen Tinubu don samun haske a kan alƙiblar da gwamnatinsa za ta ɗauka.

Sallamar dukkan manyan hafsoshin tsaro da maye gurabensu da sabbin jini, tare da naɗa Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin mashawarcin tsaron ƙasa, wanda shi ne kan gaba a naɗe-naɗen da ya yi zuwa yanzu.

Shugabancin Ecowas

A watan Yuli ne, aka zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS).

An zaɓe shi ne a lokacin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ƙungiyar karo na 63 a Bissau, babban birnin Jamhuriyar Guinea-Bissau.

Babu daɗewa kuma, sai aka samu wani juyin mulki a Nijar, inda ya aika wani ayari zuwa ƙasar don shiga tsakani.

Tafiye-tafiye

Tafiyar Shugaba Tinubu ta farko a hukumance a matsayinsa na shugaban Najeriya, ya yi ta ne zuwa Paris.

Ya bi sahun takwarorinsa daga sassan duniya zuwa Faransa don halartar taron ƙolin Paris kan sabuwar yarjejeniyar harkokin kuɗi ta duniya.

Bayan nan ya kai ziyara Guinea Bissau inda halarci taron Ecowas karo na 63, ya kuma je Nairobin ƙasar Kenya inda ya halarci taron tsakiyar shekara, karo na 5 na Tarayyar Afirka.