You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776830

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Abin da zan fi kewa a fadar shugaban ƙasa - Aisha Buhari

Uwar gidan shugaban Najeriya mai barin gado, Aisha Muhammadu Buhari Uwar gidan shugaban Najeriya mai barin gado, Aisha Muhammadu Buhari

Uwar gidan shugaban Najeriya mai barin gado, Aisha Muhammadu Buhari ta ce abin da za ta fi kewa a fadar shugaban ƙasa shi ne yawon da take yi da daddare, inda ta ce ta kan yi tattaki daga ofishin shugaban ƙasa zuwa kofar shiga fadar.

A hirarta ta musamman da BBC a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja, Hajiya Aisha Buhari ta ce kuma ya kamata a bai wa matan tsofaffin shugaban ƙasa alawus-alawus saboda irin nauyin da yake rataye a kansu, inda ta ce zai yi kyau a riƙa basu kamar yadda ake bai wa mazajensu.

Mai ɗakin shugaban Najeriyar ta ce za ta bi mijinta zuwa Daura har tsawon lokacin da zai zauna a can bayan sauka daga mulki ba wai komawa Dubai ba kamar yadda wasu ke raɗe-raɗe a faɗin ƙasar.

Ta ce abin da za ta mayar da hankali da zarar sun miƙa mulki shi ne kula da yaranta da kuma jikokinta saboda "shekara takwas da suka wuce ban samu lokacin yin hakan ba saboda mulki," in ji Aisha.

Ta ce akwai yiwuwar za ta sake buɗe makarantarta ta koyawa mutane sana'o'in hannu wanda take da lasisinsa tun kafin su hau mulki.

"Ina ganin abin da ƴan Najeriya za su fi tunawa da gwamnatin mu shi ne yawan sadakar abinci da sauransu," in ji Aisha Buhari.

Ta kuma ce za ta fi samun sukuni da kwanciyar hankali idan aka samu raguwar a irin mutanen da ke tare da ita ba kamar lokacin da suke mulki ba.