You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896677

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Abin da ya sa muka ƙi sakin Bazoum - Tchiani

Mohamed Bazoum, shugaba da anka cire a mulki Mohamed Bazoum, shugaba da anka cire a mulki

Jagoran sojojin da suka tuntsirar da gwamnatin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce akwai dalilan da suka sanya su ƙin sakin hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum.

Janar Tchiani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta gwamnati a ranar Lahadi.

Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas ko Cedeao) ta ce za ta wakilta wani ayari da zai ƙara tattaunawa da jagororin mulkin sojin na Nijar domin warware kiki-kaka da ake ciki tun bayan juyin mulkin watan Yuli.

Tun farko, Ecowas ta yi barazanr ɗaukar matakin soji a kan Jamhuriyar Nijar matuƙar sojojin suka gaza mayar da Bazoum kan mulki.

Sai dai sojojin sun ƙi bin umarnin, lamarin da ya sa ƙungiyar ta ƙi cire takunkuman da ta ƙaƙaba wa Nijar tun da farko.

Sai dai a tattaunawar da ya yi da kafar yaɗa labarai ta RTN, Shugaba Tchiani ya nuna cewa rashin tsaro da rashin tabbas na cikin dalilan da suka sa sojoji ƙin sakin hamɓararren shugaban.

A cewarsa: “Mu mun san abin da ya sa muke tsare da shi.”

Tchiani ya ce ba zai yiwu a saki Bazoum a lokacin da ƙasashen duniya ke ta kiraye-kirayen a sake shi ba, saboda barazana ta tsaro.

Ya ƙara da cewa har yanzu Nijar na cikin barazanar fuskantar hari: “Muna cikin barazanar (kawo mana) hari, muna bisa barazanar ta’addanci”.

Ba ta yiwuwa in bar shi ya fita, (idan) lokaci idan ya yi na fitar shi, zai fita.”

Yayin taron da ta gudanar a Abuja babban birnin Najeriya a ranar Lahadi, Ecowas ta ce za ta duba yiwuwar rage takunkuman da ta sanya wa Nijar, idan sojoji suka amince da mayar da mulki ga farar hula cikin ƙanƙanin lokaci.

Shugabannin ƙasashen Benin da Saliyo da Togo ne za su jagoranci tattaunawar, inda za su matsa wa sojojin na Nijar lamba don su amince da wani jadawali "mai yiwuwa kuma na ɗan lokaci" don mayar da mulki hannun farar hula.

A kwanan nan ne, Burkina Faso, da Nijar, da Mali suka amince da kafa wani ƙawancen tsaro da kuma haɗaka ta siyasa.

Takunkumai sun jefa al'ummar Nijar cikin wahala

Nijar mai yawan al'umma miliyan 27 na ƙoƙarin shawo kan mummunan tasirin takunkuman.

Ƙasashen yammacin Afirka maƙwabtan Nijar sun taƙaita cinikayya da ita da katse lantarki da kuma hada-hadar kuɗi.

Takunkuman da suka samu goyon bayan Tarayyar Turai sun kasance masu tsauri da aka ƙaƙaba wa wata ƙasa mamba a ƙungiyar Ecowas.

Da farko Najeriya da Benin ne suka fara rufe kan iyakoki, daga nan Najeriya ta sake katse wa Nijar lantarki. Sannan an dakatar da hada-hadar kuɗi tsakanin Nijar da wasu kasashen yammacin Afirka.

Kafin juyin mulkin, kasafin kuɗin Nijar na dogaro ne kacokan da tallafin da ƙasar ke samu daga waje. Amma daga baya Faransa da Amurka (da ke ba nijar tallafin lafiya da tsaro da wasu buƙatunta) sun sanar da dakatar da tallafin.

Watanni biyar bayan hamɓarar da shugaba Bazoum, al'ummar Nijar na ci gaba da kokawa kan tasirin takunkuman ga rayuwarsu ta yau da kullum.

Ƴan Nijar na shan wahala wajen samun kuɗaɗen da za su ciyar da iyali musamman manoma da makiyaya waɗanda suka fi dogaro da fitar da amfanin gona da dabbobi zuwa Najeriya.