You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776773

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Abin da ya sa ban halarci wurin rantsar da Abba Gida-Gida ba - Ganduje

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

A ranar 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da shugaban ƙasa da sababbin gwamnoni a Najeriya.

Jihar Kano na daga cikin inda aka samu sauyi a jam’iyya mai mulki, daga hannun jam’iyyar APC zuwa NNPP.

Sai dai kamar yadda aka tsammata gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje bai halarci wurin miƙa mulkin ga sabon gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Ganduje ya kasance a wurin rantsar da sabon shugaban ƙasa Bola Tinubu a Abuja, babban birnin ƙasar.

Shin mene ne dalilin da ya sanya Ganduje bai halarci taron miƙa mulki ga wanda zai gaje shi ba?

Tsohon gwamnan ya ce abin da ya sa bai halarci taron ba shi ne domin gudun tayar da husuma.

Ya ce “...idan gwamnati mai tafiya ba jam’iyyarsu ɗaya da gwamnati mai shigowa ba, ba lallai ne a halarci rantsuwar ba, domin idan an yi haka wani lokaci akan samu yamutsi saboda magoya baya.”

Ya ƙara da cewa “...demokuraɗiyyar ba ta kai yadda ka ke ganin ake gani a ƙasashen waje ba.”

A cikin tattaunawar ya kuma yi bayani kan batun neman muƙami a gwamnati mai kamawa.