You are here: HomeAfricaBBC2021 03 24Article 1213651

BBC Hausa of Wednesday, 24 March 2021

Source: BBC

Abin da ya sa aka kama sha'iri Bashir Ɗandago a Kano

Malam Bashir Dandago Malam Bashir Dandago

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta kama fittacen mawaƙin waƙoƙin yabon Annabi Muhammadu da ke Kano Malam Bashir Dandago bisa zargin zagin malaman jihar da adawa da Malam Abduljabbar Nasir Kabara.

Hukumar ta ce babban dalilin da yasa ta kama Malam Bashir Dandago shi ne ya saki wata waƙa ba tare da an tantanceta ba.

A cewar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Isma'ila Na'abba Afakallahu ya ce waƙar da Bashir Ɗandago ya fitar ya sake ta ba bisa ƙa'ida ba.

Sannan ya yi amfani da kalaman tunzuri da ɓatanci ga wasu daga cikin malaman jihar Kano, wanda ya ce yin hakan ya ci karo da dokokin hukumar tace fina-finan jihar.

Afakallau ya ƙara da cewa: "Bayan rashin kawo wa a tace ma, waƙar ta fito da wani salo na cin mutunci da cin zarafi da kuma neman kawo tayar da hankalin al'umma ko tarzoma.

"Saboda duk mutumin da ya ji wannan waƙa zai san cewa abin bai yi kama da tarbiyya da mutunci da yanayin zamantakewa da aka san Malam Bahaushe da su ba, ta wajen kyautata tarbiyya da kuma kiyaye mutuntakar juna.

"Bashir ya yi waƙa bai kawo hukuma ta tace ba kuma waƙar nan tana ɗauke da kausasan maganganun da za su iya kawo tunzuri cikin al'umma.

"Dole hukuma ta taka burki ta dauki mataki kan cin mutuncin mutane da zagin shugabanni, ai malamai shugabanni ne, akwai shugabannin da suka wuce malamai? Ai babu.

"Saboda su ne al'ummar da suke janyo mutane su nuna su zuwa ga Allah kuma su nuna musu abubuwan da suka kamata," a cewar Afakallahu.

Duk da cewa a waƙar ta Bashir Dandago bai ambaci sunan ko mutum guda ba, ya yi ta kamar zaurance ne, Afakallahu ya ce babban laifinsa shi ne ƙin neman izinin yin waƙar tun da farko.

"Ƙa'ida ta farko ita ce idan ka yi waƙa ka kawo a tace, babbar ƙa'idar da ya fara karyawa kafin a shiga ma batun mene ne a cikin wakar shi ne rashin neman a sahhale masa ya je ya yi waƙar.

"Wannan shi ne babban abu mafi muhimmanci da al'umma ya kamata ta fara fahimta.

"Kuma shi yana cikin waɗanda suka zauna suka tantance sha'iran da ke cikin wannan kwamiti a matsayinsa na wanda ake koyi da shi

Bashir Dandago dai na daya daga cikin manyan masu yabon Mazon Allah SAW a Kano, kuma daya daga cikin magoya bayan Abduljabbar Kabara, wanda kuma ya saki wakar da ake tuhumarsa da yin kalaman tunzuri da gugar zana ga wasu malamai, tare da sakinta ba bisa ƙa'ida ba.

Haka zalika lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da wani lauya mai zaman kansa Ma'aruf Yakasai ya janye daga bukatar da ya shigar gaban kotu ta hana gwamnatin Kano, yin muƙabala da Abdulajbar Nasir Kabara.

Batun muƙabalar ya ja hankulan al'umma a ciki da wajen jihar Kano, har ta kai ga wasu mutane ke nuna rashin jin dadinsu lokacin da aka dakatar da muƙabalar.

Wanda hakan ya janyo musayar kalamai tsakanin magoya bayan malaman Kano da ɓangaren Abduljabbar kan batun dakatar da muƙabalar.