You are here: HomeAfricaBBC2023 01 27Article 1703237

BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Abin da muka sani kan kashe makiyaya a Jihar Nasarawa

Hoton alama Hoton alama

Bayanai na ƙara fitowa fili game da wani ƙazamin harin jirgin sama da ya yi sanadin kashe fararen hula aƙalla 28 a yankin Doma na jihar Nasarawa a ranar Laraba.

 Lamarin ya faru ne bayan makiyayan sun karɓi shanu daga hannun hukumomin jihar Benue, tare da baro jihar domin zuwa wani wurin na daban.

 Wani taro da gwamnan jihar ya kira a ranar Alhamis, ya cimma matsayar cewa za a sada dangi da shugabannin al'ummar Fulani da harin ya shafa ga hukumomin sojin Najeriya don shigar da ƙorafinsu kan abin da ya faru.

Ana ta samun bayanai mabanbanta dangane da adadin mutanen da suka rasu game da harin.

Ga dai abin da muka sani game da harin:

Yadda harin ya faru

Jaridar PR Nigeria a ƙasar ta ruwaito cewa tun da farko sojoji sun samu bayanan da ke nuna cewa akwai wasu da ake zargin ƴan ta'adda ne sun kutsa cikin wani yanki da ke kan iyaka da Nasarawa da Benue.

Daga nan ne aka shirya samame na musamman domin yaƙar ƴan ta'adda inda aka yi rashin sa'a aka far wa makiyayan da suka je belin shanunsu a jihar Benue.

Sai dai sojoji har yanzu ba su musanta cewa su suka kai hari kan makiyayan ba.

Mutum nawa suka rasu?

Ƴan sanda a Jihar dai sun tabbatar da cewa mutum 28 ne aka yi wa jana'iza sakamakon harin.

Amma dai jaridun Najeriya suna ruwaito adadin da ya wuce haka inda ko jairdar Punch ta ruwaito gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule yana cewa aƙalla mutum 37 aka binne.

Martanin jami'an tsaro

A lokacin da lamarin ya faru, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa Maiyaki Muhammed Baba, ya tabbatar da lamarin inda ya ce sun samu labarin faruwar lamarin a ranar Laraba.

Haka ma a yayin tattaunawa da BBC, kakakin gwamnatin jihar Nasarawa Ibrahim Adra ya tabbatar da lamarin inda ya ce tuni jami'an tsaro suka ɗauki matakai ƙwarara a wurin da lamarin ya faru.

Sai dai har yanzu waɗanda ake zargi da kai harin wato rundunar sojin sama ta Najeriya ba ta fitar da sanarwa ba kuma ba ta fito fili ta yi ƙarin haske a kan zargin da ake yi mata.

Me ƙungiyar Fulani makiyaya ke cewa?

Ƙungiyar Miyetti Allah kautal hore ta nuna rashin jin daɗinta da kuma ɓacin rai game da wannan lamari inda ta buƙaci a gudanar da bincike a kuma yi adalci.

Ƙungiyar kuma ta koka game da dokar da gwamnatin jihar Benue ta saka ta hana kiwo.

Ya ce duk lokacin da aka kama saniya, sai an biya tarar naira dubu 50 kan kowace saniya.