You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1760969

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Abin da masana ke cewa a kan bugun ƙirjin Buhari na ɗaukar sojoji 60,000 a mulkinsa

Masana harkokin tsaro sun amince cewa Najeriya ba ta da isassun sojoji Masana harkokin tsaro sun amince cewa Najeriya ba ta da isassun sojoji

Ƙwararru na ci gaba da tsokaci game da kalaman Shugaba Muhammadu Buhari baya-bayan nan na cewa shirinsa na bunƙasa harkokin tsaro a Najeriya, ya cimma nasara, ciki har da ɗaukar soja 60,000 aiki a zamaninsa.

Sai dai wasu masana harkokin tsaro a ƙasar kamar Group Captain Sadiq Garba Shehu (mai ritaya) ya ce ko da yake ɗaukar sojoji guda 60,000 ƙoƙari ne, amma dai bai taka kara ya karya ba.

"Ɗaukacin ƙwararru kan fannin tsaro sun yi ittifaƙin cewa Najeriya ba ta da isassun sojoji. Ba ta da isassun 'yan sanda," in ji shi.

Ya ce a ra'ayinsa Najeriya na buƙatar ƙarin soja 60,000 ne duk shekara a halin da take ciki, maimakon 60,000 da gwamnatin Buhari ta ɗauka a cikin shekara takwas.

Don haka in ji group captain: "ƙarin da aka yi, bai isa ba".

Sadiq Garba ya ce ƙasa kamar Najeriya da ake cewa babbar yaya a Afirka, akwai bukatar idan an an samu wata tarzoma ko rigima a wata ƙasa musamman a Afirka ta Yamma, Najeriya za ta iya zuwa kai ɗauki.

Idan Majalisar Ɗinkin Duniya, a cewarsa ita ma tana neman ɗauki na dakarun kwantar da rikici, za a iya aika mata.

"To ga ka, sai ka nemi sojoji waɗanda za su ishe ka yaƙinka na cikin gida, za kuma su isa, ka je ka kai wa wata ƙasa wani ɗauki.

Tsohon sajan saman ya ce har yanzu Najeriya ba ta da yawan sojojin da suka ishe ta.

Shugaba Buhari dai ya ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu a shirin gwamnatinsa na inganta tsaro ta hanyar bunƙasa kayan aiki da gina cibiyoyin aiki da horarwa, da kuma ɓullo da tsarin kyautata walwala da jin daɗin ‘ya'yan sojojin da suka mutu a bakin aiki.

Ya bayyana haka ne a wani taron ƙaddamar da launukan rundunonin sojin Najeriya ranar Alhamis a Abuja.

Shugaban mai barin gado ya ce ya bayar da umarnin ɗaukar sojoji 60,000 aiki a rundunar sojin ƙasar, kuma wasu dubbai sun kammala karatu daga kwalejin sojojin Najeriya ta NDA, da sauran cibiyoyin nazarin tsaro.

Dakile ayyukan masu tayar da ƙayar-baya

Shugaban Najeriyar ya kuma ce lokacin da gwamnatinsa ta karɓi ragamar mulki, harkokin tsaron ƙasar cike suke da ƙalubalen 'yan ta-da-ƙayar-baya, amma yanzu a cewar sa abin farin ciki shi ne al’amura sun inganta matuka.

'Ina kuma yin alfahari da kara nuni da cewa mun samu gagarumin cigaba a fannin yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, na Boko Haram, da na yankin Neja Delta, da masu satar ɗanyen man fetur, da masu satar mutane don neman kuɗin fansa da sauran masu aikata miyagun laifuka a kasar,' in ji shi.

Matsalolin hare-hare da kashe-kashe, da kuma sace-sacen jama’a don neman kudin fansa, da ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji a wasu sassan Najeriyar musamman a yankunan arewa maso gabashi da arewa maso yammacin kasar abu ne da ya dade yana ci wa jama’a da kuma hukumomi tuwo a kwarya.

Sannan sun yi sanadin salwantar rayukan jama’a da dukiya mai tarin yawa.

Inganta ayyukan rundunar sojin ƙasar

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta samu gagarumar nasarar sauye-sauye wajen inganta rundunar sojin Najeriya ta ɓangaren ba da horo, da ayyukan soji, da ƙara yawan dakaru da ma’aikata, da biyan diyya, da ayyukan kula da lafiya.

‘’Waɗannan sun kuma haɗa da samar da wuraren zama, da ƙara yawan dakarunmu, da ayyukan gyare-gyare, don haka cigaban da aka samu a waɗannan ɓangarorin sun ƙarfafa gwiwa tare da inganta ayyukan sojojinmu wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda tsarin mulki ya tanada,’’ in ji shi.

Shugaba Buharin, ya kuma yi nuni da cewa yawan sojojin Najeriya a watan Mayun 2015 ya ragu matuƙa, inda ya ƙara cewa amma bayan shekaru bakwai ya yi gagarumar ƙaruwa, abin da ya sa ta samu matsayi na huɗu a rundunonin sojin ƙasashen Afirka a kan matsayi na bakwai da take da shi a 2015.

Ya kuma ce tsare-tsaren da gwamnatinsa ta ɓullo da su kamar na ware kasafin kuɗi na shekara-shekara ga rundunar soji daga 2020 da 2022 kaɗai, ya ba da damar sayen ɗaruruwan motocin sulhu da za su tabbar da kariya daga yi wa dakarun ƙofar rago.

Haka an sayi motocin ɗaukar dakarun, da tankokin yaƙi da makamantansu da ƙara a kan waɗanda aka riga aka saya a baya.

“Daga shekarar 2017 zuwa 2022, an samar da sabbin motocin yaƙi da na ayyuka na musamman tare da bindigogin atilare, da na igwa, da ƙananan bindigogi da sauran makamai.

Tabbas hakan ya kara yawan kayan aikin rundunar soji mafi girma da aka samu tun a 2015.’’

Hakan in ji shugaba Buharin ya kara wa dakarun azamar fuskantar ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka a fagen daga musamman a yankin arewa maso gabas wanda ya haifar da sake kwace tarin yankunan da ‘yan ta’addan Boko Harama suka kwace a baya.

Kyautata jin daɗin rayuwar dakarun ƙasar

Ta ɓangaren kyautata jin daɗin dakarun ƙasar kuwa, a cewar shugaban Najeriyar, gwamnatinsa ta yi gagarumim garanbawul a fannin inganta tsare-tsaren biyan albashi da alawus-alawus na dakarun don karfafa musu guiwar gudanar da aikinsu.

“Har ila yau, mun yanke shawarar kula da jin dadi da walwalar iyalan sojojin da suka mutu - kananan yara 50,000 da matan dakarun da suka rasa rayukansu a yayin yi wa kasar su aiki, kuma yanzu haka yaran na cikin masu amfana da tallafin karat una Rundunar Sojin kasar tun daga shekarar 2015 har ya zuwa yanzu,’’ ya bayyana.

Ta ɓangaren ayyukan gine-gine kuwa, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari na samar da gidaje da wuraren zama da sauran kayyakin more rayuwa ga dakarun, kana a yayin da yawan sojojin ke karuwa, kuma an yi yunkuri na musamman wajen gina sabbin barikokin soja tare da gyara tsofaffin da ake da su.

“A halin da ake ciki, an gina sabbin ɗaruruwan gidaje kana an gyara dubban tsofaffin gidajen sojojin a wurare daban-daban na kasar tsakanin shekarar 2016 da 2022,’’ in ji Buhari.

Ya kuma kara da cewa “Yanzu haka kuma, ana gudanar da gagrumin ayyukan gine-ginen a sabuwar barikin sojin Muhammadu Buhari da ke Abuja, da sauran barikokin soji don kara wa dakarun kwarin gwiwa.