You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836290

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Abin da Faransa ke yi mana, tsabagen katsalandan ne - Sojojin Nijar

Abdourahmane Tchiani, shugaban sojojin Nijar Abdourahmane Tchiani, shugaban sojojin Nijar

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi a kan yiwuwar shiga matsalolin jin ƙan ɗan'adam a Nijar, bayan sabbin shugabannin mulkin sojin ƙasar sun dakatar da ayyukan hukumomin Majalisar, a abin da suka kira yankunan da sojoji ke ayyuka na musamman.

Sojoji sun ƙwace mulki a ƙarshen watan Yuli a ƙasar mai fama da rikice-rikicen 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Mutane sama da miliyan uku ne tun tuni ke fama da yunwa a Nijar, kuma tun bayan juyin mulkin an samu hauhawar farashi da kashi 20 cikin 100.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ke cewa "ranta ya ɓaci" da kalaman Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, wanda a ranar litinin ya nanata goyon bayan gwamnatinsa ga hamɓararren shugaban ƙasar, Bazoum Mohamed.

Mai magana da yawun gwamnatin Nijar ya bayyana lamarin da "tsabagen katsalandan".

Ita dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana ƙoƙarin tuntuɓar shugabannin juyin mulkin Nijar, bayan dakatar da ayyukan hukumominta da na sauran hukumomin ba da agaji.

Mai magana da yawun majalisar, Alessandra Vellucci ta faɗa wa manema labarai a Geneva cewa "Mun ga rahotanni.

Muna ƙoƙarin tuntuɓar hukumomi da ke mulki a Nijar don inganta fahimtar abin da hakan yake nufi da illolin hakan ga ayyukan jin ƙan ɗan'adam.

Kalamanta na zuwa ne bayan ma'aikatar harkokin cikin gida da maryacen ranar Alhamis ta ba da sanarwar cewa an dakatar da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin ba da agaji da sauran hukumomin duniya daga aiki a yankunan da sojoji ke gudanar da ayyuka na musamman.

Sanarwar ba ta ce ga ayyukan da matakan suka shafa ba, amma ta ce an ɓullo da matakan ne "saboda yanayin tsaro da ake ciki a yanzu".

"Duk wasu aikace-aikace da kuma zirga-zirga a yankunan ayyuka na musamman an dakatar da su na wani ɗan wani lokaci," a cewarta.

Sabbin shugabannin mulkin sojan Nijar sun ƙwace iko a wani juyin mulki na ranar 26 ga watan Yuli, lokacin da dakarun soji suka hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed.