You are here: HomeAfricaBBC2023 09 19Article 1847267

BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

AC Milan da Newcastle sun tashi ba ci a Champions League

Olivier Giroud Olivier Giroud

AC Milan da Newcastle United sun tashi 0-0 a wasan farko a rukuni na shida, na gasar Champions League da suka buga ranar Talata a Italiya.

Wasan farko da Newcastle ta buga a gasar zakarun Turai, tun bayan shekara 11, amma karon farko a Champions League bayan shekara 20.

Milan ta sa matsi don cin ƙwallo karo da dama a fafatawar, kuma tun bayan shakarar 2003/04 ta zama ta shida da ta buga ƙwallo kai tsaye zuwa raga sau bakwai, ba tare da ƙwallo ta faɗa raga ba.

Kuma ita ce ta farko tun bayan da hakan ya faru ga Chelsea a fafatawa da Malmo cikin Nuwamban 2021.

Milan ta yi rashin nasara a ƙarshen mako a hannun Inter Milan da ci 5-1 a gasar Serie A, karawar mako na huɗu.

Ita kuwa Newcastle United, wadda aka doke wasa uku a jere a Premier League ta yi nasarar cin Brentford 1-0 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wannan shi ne karon farko da aka kara a gasar zakarun Turai tsakanin Milan da Newcastle United a tarihi.

Milan tana da Champions League bakwai, amma rabonta da cin kofin tun bayan 2006/27, ita kuwa Newcastle ba ta taɓa ɗaukar kofin ba.

Ranar 4 ga watan Oktoba, Newcastle za ta karɓi baƙuncin Paris St Germain, inda Milan za ta ziyarci Borussia Dortmund a Jamus duk dai a ranar.