You are here: HomeSports2021 03 24Article 1213678

BBC Hausa of Wednesday, 24 March 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Lloris, Wijnaldum, de Gea da Ramsey

Cristiano Ronaldo, zai koma Real Madrid in har kungiyar ta Sifaniya ta nemi dawo da dan wasan na Juventus dan Portugal mai shekara 36, kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.

Manchester United na duba yuwuwar sayen dan bayan Sevilla Jules Kounde, mai shekara 22, da Pau Torres, mai shekara 24, na Villareal. Yan wasan bayan biyu na gasar La Liga su ne a gaba-gaba da United ke fatan samu a bazaran nan kamar yadda labarin ya bayyana daga kafar 90 min.

Haka kuma Manchester United din ka iya neman golan Tottenham Hugo Lloris, mai shekara 34, domin maye gurbin David de Gea, yayin da Spurs din ita kuma take harin mai tsaron ragar Lille Mike Maignan mai shekara 25. L'Equipe ce ta ruwaito daga jaridar Mail.

Manchester City na sha'awar sayen dan wasan tsakiya Borussia Monchengladbach Denis Zakaria, mai shekara 24.

Man City na nazari a kan dan wasan na kasar Switzerland domin maye gurbin Fernandinho a bazaran nan. Sky Sports ce ta ruwaito labarin daga Manchester Evening News.

Ga alama Liverpool za ta rasa Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, ga Barcelona, kamar yadda rahotanni ke ta bayyana cewa akwai yarjejeniyar hakan a kan dan wasan na Holland tun kafin kungiyar Premier ta saye shi a baya.

Tuni ma Liverpool din ta fara nazarin dauko Aaron Ramsey dan Wales daga Juventus, domin rufe gurbin. CalcioMercato ce ta labarto daga jaridar Star

Ramsey's Ita kuwa tsohuwar kungiyar Ramsen wato Arsenal tana nazari ne kan dauko dan wasan tsakiya na Real Betis, dan Argentina Guido Rodriguez, mai shekara 26. Mundo Deportivo ce ta dauko labarin daga jaridar Metro

Zakarun Turai kuma na Jamus, Bayern Munich suna tattaunawa da Lucas Vazquez mai shekara 29, wanda yarjejeniyarsa da Real Madrid za ta kare a watan Yuni

Tsohon dan wasan bayan na Sifaniya zai kasance ba tare da wata kungiya ba a karshen wa'adin nasa da Real Madrid, kamar yadda labarin ya bayyana a AS.

Shi kuwa tsohon dan bayan Real Madrid din Fernando Hierro yana son ganin dan bayan Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 34, ya sabunta zamansa a Madrid din kuma ma har ya yi ritaya a kungiyar, in ji jaridar Marca.

Kociyan Everton Carlo Ancelotti yana son dauko tsohon dan wasansa a Napoli Kalidou Koulibaly, kamar yadda labarin ya bayyana a Talksport

Ancelloti na ganin dan wasan bayan dan Senegal mai shekara 29, zai yi masa amfani sosai a kungiyar ta Premier.

AC Milan ta ji dadin aron dan wasan baya dan Ingila defender Fikayo Tomori mai shekara 24, abin da ya sa take son ta nemi Chelsea ta sakar mata shi dindindin, kamar yadda labarin ya bayyana a Goal.

Burnley da Newcastle kuwa suna sha'awar dan bayan West Bromwich Albion ne Kyle Bartley.

Kungiyon biyu suna harin dan Ingilar ne mai shekara 29, ganin cewa shekara da ya ce ta rage masa a kungiyar, in ji Telegarph.