You are here: HomeAfricaBBC2024 05 10Article 1930173

BBC Hausa of Friday, 10 May 2024

Source: BBC

Me ya sa iyalan masarautar Birtaniya ke ziyara a Najeriya?

Yarima Harry da Meghan a Abuja ranar 10 Mayu, 2024 Yarima Harry da Meghan a Abuja ranar 10 Mayu, 2024

Yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan sun isa Najeriya inda za su yi ziyarci musamman biranen Abuja da Kaduna.

Babban maƙasudin ziyarar ta kwana uku shi ne domin halartar bukukuwan cika shekara 10 da samar da wasannin ‘Invictus Games’ – na sojojin da aka raunata a fagen daga.

Yarima Harry ɗaya ne daga cikin waɗanda suka samar da bikin wasannin a shekara ta 2014.

Invictus Games gasar motsa jiki ne da ta ƙunshi abubuwa daban-daban wadda aka ƙirƙiro domin sojoji waɗanda suka samu rauni a wurin yaƙi.

Sojojin da ke kan aiki da kuma wadanda suka yi ritaya duk suna iya fafatawa a gasar.

Yarima Harry ya yi sha’awar samar da gasar ne bayan ya lura da ya kalli yadda aka gudanar da gasar ‘Warrior Games’ a ƙasar Amurka cikin shekarar 2013, inda ya ga yadda wasannin motsa jiki ke taimakawa wajen inganta lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa.

‘Invictus’ kalma ce da ta samu asali daga harshen Latin, wadda ke nufin ‘waɗanda ba a cin galaba a kansu’.

A lokacin ziyarar tasu, Harry da Meghan za su gana da Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Christopher Musa a ranar Juma’a, inda za su ziyarci wata makaranta a tare, kafin su gana da sojojin da aka yi wa rauni.

Daraktar wasannin motsa jiki a shalkwatar tsaro ta Najeriya, Abidemi Marquis ta ce “Za su zarce zuwa garin Kaduna inda za su je Asibitin sojoji ta 44, inda wasu sojojin da suka samu raunuka a fagen daga suke samun kulawa. Kuma za su yi amfani da damar wajen ziyartar gwamnan jihar Kaduna”.

Ta kuma ƙara da cewa “a ranar Asabar za yi wani wasan sada zumunta tsakanin tawagar babban hafsan tsaron Najeriya da kuma tawagar yarima Harry. Yariman da mai ɗakinsa za su yi amfani da damar wajen tattaunawa da sojojin da suka ji rauni da sauran dakarun Najeriya”.

A ranar Lahadi kuma ma’auratan biyu za su tafi biurnin L;egas domin kai ziyara a wata gidauniyar da suke tallafa mawa, inda za su ƙaddamar da filin wasan kwando da suka gina a makarantar.

Haka nan kuma za su gana da gwamnan jihar ta Legas.

Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta ce “ziyarar na gudana ne bisa ga gayyatar Babban hafsan hafsoshin Najeriya, kuma ziyara ce ta ƙashin-kai ba da sunan gwamnati ba.”

Marquis ta kuma ce mai ɗakin Haryy, wato Meghan ta zaƙu ta kai ziyara Najeriya kasancewar bincike ya nuna cewa kashi 43 cikin ɗari na tsatsonta ya samo asali ne daga Najeriya.

Duk da cewa gasar motsa jiki ta dakarun da aka raunata a fagen daga ta Invictus Games tana cika shekara 10 da samuwa ne a yanzu, amma sai a shekarar 2023 ne Najeriya ta halarci gasar a karon farko, wadda aka gudanar a ƙasar Jamus.

Hakan ya sanya tawagar Najeriya ta zamo ta farko da ta shiga gasar daga nahiyar Afirka.

A gasar ta farko da Najeriya ta halarta, tawagarta ta samu nasarar lashe lambar zinare da tagulla.