You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283032

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Ɓaro-ɓaron Macron zai iya kawo koma baya ga alakar Faransa da Afrika

Shugaban Faransa Emmanuel Macron Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kara daukar magana gaba-gaɗi a matsayin wani mataki na tafiyar da diflomasiyya, a wannan karon yana magana ne da shugaban Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya( JAT).

Ya bayyana Faustin-Archange Touadéra a matsayin "mai masaukin" kungiyar Wagner, wata tawagar sojin Rasha da ke taimaka wa gwamnatin Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya wajen yaki da 'yan ta da kayar bayan da suke zamar wa kasar barazana.

Paris ta nuna ɓacin ranta da wani sako da ke nuna ƙin jinin Faransa da wani makusanci shugaban Touadéra ya wallafa, da ke tuno da wani ɓacin rai kan kasar da ta yi musu mulkin mallaka.

Shiga tsakiyar da Faransa ta yi da kuma sojojin Afrika a 2013, ya ceci Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya daga fadawa rikicin da zai janyo kiyan kiyashi ga fararen hula, suka tabbatar da an dawo tsarin dimokradiyya da aka yi zaben karkashinsa ya kuma bai wa Mr Touadéra damar lashe zabe a 2016.

Sai dai kasar ta dogara ne kan sojin rasha wajen taimaka mata, a baya ta sanya hannu kan yarjejeniya da Rasha domin ba ta damar hakar zinare da gwal da makamashin uranium.

Matakin da ya janyo fargaba da Moscow tare da janyo bacin rai ga masu adawa da Faransa, wannan ya sanya Mr Macros janye tallafin da yake bai wa kasar JAT.

Macron cikin wata hira da ya yi da jaridar Journal du Dimanche (JDD) ya ce akwai bukatar a fito ƙarara a yi gargadi.

Wannan maganganun nasa sun yi daidai da wani mataki da ya dauka wanda ba na kai tsaye ba, duk da cewa gwamantin Mr Toudera ta ce ita tsare-tsarenta da ma'aikatar tsaron Rasha ne ba da Wagner ba.

Sai dai ba kawai shugaban JAT wannan gugar zana ta Marcon suka nufa ba.

Ya kuma yi wa Mali gargadi - inda mataimakin shugaban kasar Kanar Assimi Goita ya kara aiwatar da wani sabon juyin mulki tare da hambarar da shugaban kasar da firaiministansa - faransa ta ce za ta janye sojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar matukar aka ragwantawa masu tsattsauran ra'ayin kishin Islama.

An ta yaɗa wannan tattaunawa da ya yi da JDD a kasashen rainon Faransa. Tabbas Macron ya san yadda zai rika jan hankalin mutane.

Tsarin Macron na 'jiji da kai'

Macron na fuskantar matsalolin Afrika a gabansa, amma da irin wannan ɓaro-ɓaron da yake yi, ba ya tsoron ya bayyana abin da ke ransa a bainar jama'a domin kawo sauyi.

Wannan tabbas zai iya kawo sakamako - kamar yadda aka gani a ziyarar da ya kai Rwanda a makon jiya inda ya bayyana ƙarara cewa gwamnatin Faransa a wancan lokacin ta gaza kare kisan kiyashin da aka yi a kasar a 1994 yadda ya kamata, a wani mataki na sake gina alaƙar diflomasiyya da za ta kawo ƙarshen tarihin nan maras daɗi.

Mayar da kayayyakin tarihin da aka sace

Wadannan shekaru hudun sun nuna kwarewa da yadda ya shirya tsaf domin magance wasu matsaloli daɗaɗɗu da kuma samar da sabbin hanyoyin alaka.

Macron ya kaddamar da wasu kwamiti masu zaman kansu guda uku domin su gabatar masa da rahoton kan halayya: game da yadda aka zubar da jini kan rikicin samun 'yancin Algeria.

Sannan akwai batun kisan kiyashin Rwanda da kuma maganar yadda za a mayar da kayayyakin al'ada da tarihi da aka kai Faransa tun lokacin mulkin mallaka.

Gwamnatinsa ta gano gazawar Faransa ne ta dalilin rahoton Vincent Duclert wanda aka wallafa baki daya.

Bayan karbar rahoton masanin tarihin nan Benjamin Stora kan Algeria a watan Janairu, shugaban Faransa ya ce zai kafa wani shiri da zai sake sabunta alaka tsakanin kasashen biyu karkashin kulawar Farfesa Stora.

Masu suka na ganin cewa Mr Macros bai gama fahimtar abin da ake mukata ba, amma aiwatar da shawarwarin da aka bashi kan Algeria zai iya kawo karshen rikicin siyasar da kasashen arewacin Afrika ke fama da shi.

Tuni aka fara mayar da kayyyanin tarihin, an mayar wa Senegal da wani takobi dai wani kambun sarauta da aka mayar Madagascar, sannan kuma ana shirin yadda za a mayar da wasu kayan guda 26 zuwa Benin.

Rikici kan amfani da 'kudaden mulkin mallaka'

Faransa da Tarayyar Turai, sai sun kara mayar da hankali kan yadda za a cimma alakar ta fuskar siyasa, cigaban tattalin arziki don taimakawa daga 0.55 cikin 100 a 2022, da ci gaba da zaman sojoji musamman domin taimaka wa a kawo karshen kungiyoyin masu ta da kayar baya a yankin Sahel - da kudu hamadar Sahara - da suka hadar da Mali Chadi Nijar Burkina Faso da kuma Mauritania.

Amma yadda yake kokarin sabunta alakar Faransa, a gefe daya kuma yana fito da yadda Paris ta yi barna a lokacin mulkin mallaka.

Idan muka koma 2017, Macron ya ce idan kasashen yammacin Afrika suka zabi su daina amfani da Saifa Faransa za ta goyi bayansu.

An kuma sanar da matakin farko na sassauta matin lamba kan hakan a watan Disambar 2019.

A yankin Sahel wasu na sukar Faransa da barin dakarunta domin muradinta na tattalin arziki.

Faransa ta zuma jari mai yawa a hakar ma'adanin uranium a Nijar - sai dai kasashen Canada da Rasha da Astralia da kuma kamfanonin Burtaniya ne suka mamaye bangaren hakar Zinare a kasashen Sahel.

Macron na son sauya kallon da ake yi wa Faransa ne a Afrika, sai dai akwai wasu abubuwa na san rai da sai an fara kawar da su da yaren da mutane za su gane.

Sai dai sauya hakan ba zai taba zama da sauki ba.