You are here: HomeAfricaBBC2021 03 28Article 1217305

BBC Hausa of Sunday, 28 March 2021

Source: bbc.com

Zai yi wuya a iya kaucewa kara kudin mai a Najeriya – Masana

Masana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da furucin da Shugaban Kamfanin Mai a Najeriya, Mele Kyari, ya yi cewa gwamnati na kashe wuri na gugar wuri har naira biliyan 120 a kowane wata a matsayin tallafin man fetur.

Mele Kyari wanda ya bayyana hakan ya ce kamfanin ba zai iya ci gaba da biyan wadan nan makudan kudade ba, saboda haka dole ne 'yan Najeriya su hakura su sayi man fetur bisa yadda farashin ya kama.

Dr Ahmed Adamu, masanin tattalin arziki da ya shafi man fetur a jami`ar Nile da ke Abuja ya shaida wa BBC cewa zai yi wuya gwamnatin ta dore da biyan makudan kudaden a matsayin tallafin mai saboda irin dawainiyar da ke kanta da kuma yadda bukatar mai ke kara karuwa a kasar.

"Man da muke sha a Najeriya duk rana muna shan akalla lita miliyan 75 wanda a kowace lita idan aka duba banbanci tsakanin yadda ake saida shi a kasuwa da yadda ya kamata a sayar a kasuwa inda ba hannun gwamnati, tallafin da gwamnati take bada wa a kan kowace lita N47". in ji masanin.

A cewarsa, gwamnati ta yi gaggawar cire tallafin mai ba tare da duba abubuwan da suke faruwa ba. Ya ce tallafin man fetur abu ne da ya zama dole a Najeriya saboda akwai matakan da ya kamata a ce sai an samar da su sannan a cire tallafin.

Zai yi wuya a kaucewa karin farashin mai a Najeriya ...

Masanin tattalin arzikin da ya shafi man fetur ya ce abu ne mai wuya ba a samu karin farashin mai ba a kasar "duk da cewa ya danganta da wasu abubuwa".

Ya ce lamarin ya danganta da farashin man fetur a kasuwar duniya, "idan farashin danyen man fetur ya ci gaba da hauhawa kamar yadda yake a baya-bayan nan, kudin da ake shigo da tataccen mai zai kara tsada kuma idan ya kara tsada nauyin tallafin da gwamnati ke badawa zai yi mata yawa har lokacin da za ta ce ta gaza toh yan Najeriya sole su sa yi mai da tsada".

A cewarsa, idan kuma aka samu farashin danyen mai a duniya ya yi kasa, toh kudin da ake shigo da tataccen mai zai ragu.

Yadda gwamnati za ta rage radadin janye tallafin mai

Dr Ahmed Adamu ya ce abu na farko da gwamnati za ta yi domin saukaka wa yan Najeriya shi ne maido da tallafin man amma na wucen gadi kafin matatar man Dangote ta fara aiki.

Sai dai ya ce ko da matatar man ta Dangote ta fara aiki, sai an tabbatar da an samu yarjejeniya ta yadda za a rika sayar da tataccen man a cikin gida da arha ta yadda ita ma gwamnatin za ta tallafa wa matatar man ta Dangote don sayar da man a cikin Najeriya kuma ya rika sayar da man da kudin kasar.

Join our Newsletter