You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283041

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

'Yan sandan Najeriya sun yi arangama da 'yan IPOB a kudancin kasar

Rundunar 'yan sanda a jihar Imo a kudu maso gabas ta ce ta kashe wani babban kwamandan 'yan a-ware na ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa ƙasar Biafra.

Ta ce an kashe Joseph Uka Nnachi wanda aka fi sani da suna Dragons ne a jiya Lahadi lokacin da suka yi yunƙurin far wa hedikwatar 'yan sanda a birnin Owerri.

A jihar Delta ma 'yan bindiga ne suka ƙona wani ofishin 'yan sanda a ƙaramar hukumar Ndokwa ta gabas tare da ƙona wata mota, ko da yake babu rahoton wanda ya rasa ran shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo SP Bala Elkana ya fadawa BBC cewa 'yan bindigar waɗanda 'yan kungiyar IPOB ne, sun shirya kai hare-hare kan manyan gine-gine gwamnati ciki har da hedikwatar 'yan sanda.

Sannan yace maharan sun yi kokarin shiga hedikwatar ne cikin wata farar mota, amma da haɗin guiwar sauran jami'an tsaro suka murkushe yunkurin da safiyar ranar Lahadi inda ya tabbatar da kashe mutum biyar ciki har da wani madugun 'yan awaren IPOB.

''An yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaron mu da 'yan IPOB, Allah ya ba mu sa'a mun kashe mutum 5 an kama wani guda an kuma kama makamai ciki har da AK47 guda 4 da wasu makamai guda 10.

Sa'ar da muka yi ita ce babban jagoransu a jihar Imo da ake kira Dragon, an jima ana neman shi amma sai yanzu aka samu nasarar kashe shi saboda yawancin dukkan hare-haren da suke kai wa jami'an mu a nan jihar Imo shi ne ya ke kitsa kai su.

Sannan jami'anmu sun kai samame maboyar 'yan IPOB, tare da kubutar da wata jami'armu mai mukamin Sajen da sukai garkuwa da ita a kwanakin baya, sun rike ta ne domin amfani da ita wajen nuna musu gidajen ma'aikata domin su kashe su,'' inji Elkana.

A can kuwa jihar Anambra wani mutum da ke fataucin shanu zuwa kudancin Najeriya ne, ya ce wasu 'yan bindiga sun buɗewa motarsu wuta a dai-dai mahadar Oba a birnin Onitcha, mutum biyu aka kashe a wannan lokacin, sannan mutanen garin sun wawashe shanun baki daya.

BBC ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra DSP Ikenga Tochukwu yace ba su sami labarin harin ba, sai dai yayi karin haske game da makamancinsa da ya auku a karshen mako na wani bidiyo a internet da ya nuna shanu na cin wuta cikin wata babbar mota a jihar, inda yace rundunar tana gudanar da bincike don gano gaskiyar abinda ya auku.

A jihar Delta da ke kudu-maso-kudu kakakin rundunar 'yan sandan jihar ne DSP Edafe Bright, ta waya ya shaidawa BBC jami'ansu sun kai farmaki maɓoyar wasu masu satar mutane a ranar Lahadi, inda yace sun kashe mutum shida da kuma kwato bindigogi da alburusai masu tarin yawa.

Sai dai a gefe guda, DSP Bright ya tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun cinnawa wani ofishin 'yan sanda na Ashaka wuta a karamar hukumar Ndokwa ta gabas tare da kona wata mota guda.