You are here: HomeAfricaBBC2021 07 22Article 1315021

BBC Hausa of Thursday, 22 July 2021

Source: www.bbc.com

Yadda rikicin Darfur na baya baya nan ya raba dubbai da muhalinsu

Khamisa Juma Ishag Abaker na cikin wadanda suka rasa muhallin sun sanadiyar yaki Khamisa Juma Ishag Abaker na cikin wadanda suka rasa muhallin sun sanadiyar yaki

Shekara biyu bayan juyin juya halin da aka yi a kasar Sudan, dubban mutane sun rasa matsugunansu ya yin da ake cigaba da fuskantar tashin hankali a yankin Darfur.

Mazauna yankin da dama sun rika fatan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma za ta kawo karshen rikicin da ya kwashe tsawon shekaru goma , sai dai akasin haka ne

Khamisa Juma Ishag Abaker mai shekara talatin da biyar ta zauna akan wani kango da a baya gidanta ne.

"Gida na nada lambu da kofa. Ina kwanciya a karkashin bishiya. Ina yi wa 'yayana girki'

Wannan shi ne karo na farko da ta koma Krinding wanda wani gari da ake tsugunar da waadanda suka rasa gidajenu u bayan rikicin da aka yi a watan Janairun ya raba dubban mutane da muhalinsu kuma daruruwa sun rasa rayukansu

"Sun kona dukkan gidajen. Mun yi kokarin guduwa kan titi, amma sun harbe dan uwana. Ya fadi ne kuma a lokacin da yake kokarin tsayawa, sai suka sake harbe shi - suka kashe shi a gabana. Na yi kuka sosai …Ba na gani kyau da idanuna a yanzu."

Yanzu tana rayuwa cikin kunci a cikin ajin wata makaranta da ke El Geneina, babban birnin jihar yammacin Darfur, ta na fama wajan kulawa da iyayenta marasa lafiya da kuma 'yayantat.

''Ba mu da kudi. Ba mu da katifa da matashin kai ko bargo….Ba ni da komai. Na zura ido ne kawai, na kasa yin komai''.

Madam Abaker ta dora alhakin hare haren akan rundunar tsaro ta musaman da gomnati kasar domin tabattar da tsaron lafiyar farar hula. Ta na jin tsoron komawa gida

Ms Abaker ta ce kungiyar mayakan sa kai na [RSF]'i da gwamnati ta dorawa alhakin kiyaye rayukan fararen hula, ita ce ke kai hare-haren.

''Zamu koma gida idan dakarun kasashen duniya suka zo amma ba za su yi haka ba.''

Mazauna yankin da daman a kewar sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da tarayyar Afrika watau UNAMID .

Bayan shekaru 13 suna aikin wanzar da zaman lafiya a yankin , kwararu sun ce janyewar da suka rika yi a hankali tun daga watan Disembar bara ta san a samu karuwa a yawan rikice rikice

Sojojin Sudan dubu ashirin da aka yi alkwarin zaaa tura, har yanzu ba su iso ba.

Yada rikicin Darfur ya samo asali

A shekarar 2003 ne yaki ya barke a yankin Darfu bayan da mayakan wata kabilar bakar fata suka yi wa shugaba Omar Al Bashir da larabawa suka fi rinjaye gomnatinsa tawaye. Bashir ya mayar da martani ta hanyar ba mayakan Larabawa da ake kira Janjaweed makamai wadanda suka rika kai wa kabillun da ba larabawa ba hari.

Dubban mutane sun hallaka ya yinda an lalata daruruwan kauyuka. A shekarar 2019 ne aka kifar da gomnatinsa sakamkon zanga zangar da ta nemi ya sauka daga kan mulki. Shekara daya bayan juyin juya halin sabuwar gomnatin rikon kwarya ta sojoji da farar hula ta sanya hannu akan yarjejreniyar zaman lafiya da wasu kunyoyin yan tawaye.

Mazauna yankin sun yi ammanar cewa za ta bude sabon babi wajan samun kwanciyar hankali sai dai kawo yanzu tashin hankali da ya soma a shekarar 2018 na cigaba da tasiri a yankin

Sakamakon haka mutun sama da dubu 150 sun rasa matsugunansu a cewar alkaluman hukumar kaura ta duniya

A farko watan Yulin da ya gabata mutum ashirin suka rasa rayukansu a rikici mai nasaba da ka kabilanci da ya faru a wani wuri mai nisan kilomita 60 da gabashin El Geneina.

Daya daga cikin kaidojin yarjejeniyar zaman lafiya a yankin shi ne hadewar mayakan RSF a cikin rundunar sojin Sudan.

Sai dai komandan kungiyar Mohammed Hamdan wanda shi ne mataimakin shugaban kasa ya fito fili ya ki hadewa da sojojin kasar.

Masana sun yi ammanar cewa wannan na kawo cikas ga tsarin samar da zaman lafiya wanda yake shafar mazauna yankin da rikicin ya daidaita