You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225537

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Yadda ƴan sanda suka kashe wani ƙasurgumin ɗan fashin daji a Zamfara

Jihar Zamfara ta na arewa maso yammacin Najeriya Jihar Zamfara ta na arewa maso yammacin Najeriya

Ƴan sanda a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun kashe wani kasurgumin dan fashin daji a jihar lokacin da ya jagoranci kai hari kan wani ƙauye a yankin Maradun.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar SP Muhammad Shehu wanda ya sanar da hakan cikin wata sanarwa, ya ce an kashe madugun 'yan fashin ne yayin wasu hare-haren da jami'ansu suka kai kan 'yan fashin dajin da suka ƙi karbar tayin sulhu.

Duk da cewa sanarwar ƴan sanda ba ta fadin sunan wanda aka kashen ba, amma ta ce ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Maradun da maƙwabtansu.

"Nan gaba kaɗan za mu faɗi sunansa," amma babban ɗan ta'adda ne kuma mun kashe shi," in ji SP Shehu.

Ya ce dalilai na tsaro ne suka sa ba za su bayyana sunansa ba.

"A ranar 4 ga watan Afrilun 2021, jami'an da aka tura yin sintiri ƙarƙashin rundunar Operation Puff Adder a ƙauyen Tsibiri kusa da dajin Sububu a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Maradun sun far wa wasu ƴan fashi da aka yi amannar suna kan hanyarsu ta kai hari ƙauyen ne.

"Da ganinsu sai suka buɗe wa jami'an ƴan sandan wuta inda nan da nan su kuma suka mayar da martani. A sakamakon haka aka kashe ɗan fashi ɗaya yayin da sauran suka tsere cikin daji da raunuka," in ji sanarwar.

A baya-bayan nan ne shugaban ƴan sandan Najeriya ya tura ƙarin jami'an tsaro da aka aika da su dazuzzukan jihar zamfara don su yaƙi ƴan bindigar da suka ƙi rungumar tsarin zaman lafiya.

"Wannan tsari shi ne na Opertaion puff Aeder. Dama an tura su Maradun shi ne suka samu bayanan cewa ƴan ta'adda sun fito daga Sububu don kai hari.

"Sai jami'an namu suka tashi tsaye suka tunkare su suka kora sauran bayan kashe mutum ɗaya," in ji mai magana da yawun ƴan sandan jihar.

Ya ƙara da cewa an samu bindigarsa ƙirar AK47 da babur ɗinsa da ake amfani da shi wajen kai irin wadannan hare-haren da kakin sojoji da kuma layu.

Abu huɗu a taƙaice kan ƙasurgumin ɗan ta'addan

  • Yana cikin manya-manyan ƴan ta'addan da suka addabi yankin ƙaramar hukumar Maradun da kewaye


  • Ya taka rawa sosai wajen kawo rashin zaman lafiya, wanda idan ba haka ba, ba zai yi jagorancin ƴan uwansa wajen zuwa su tayar wa da mutane hankula ba


  • Ya fito daga yankin dajin Sububu wanda ya yi ƙaurin suna wajen zama maɓoyar ƴan ta'adda. Yana cikin masu addabar yankin


  • Yana cikin waɗanda suka ƙi yarda da yin sasancin da gwamnatin jihar Zamfara ta shirya.