You are here: HomeAfricaBBC2021 03 09Article 1199686

BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Yadda aka kuɓutar da mahaifin ɗaya daga cikin ƴan matan Jangebe daga hannun ƴan fashin daji

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle

Gwamnatin Jihar Zamfara a Najeriya ta sanar da kuɓutar da ƙarin mutum 10 daga hannun ƴan fashin daji ciki har da mahaifin ɗaya daga cikin ƴan matan makarantar Jangebe da aka kuɓutar.

Gwamnatin ta ce an yi nasarar kuɓutar da mutanen ta hanyar amfani da ƴan fashin dajin da gwamnatin ta ce ta yi sasanci da su kuma ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Tun farko dai yarinyar ta bayyana cewa ta ga mahaifinta a lokacin da aka shigar da su daji inda rahotanni suka ce mahaifin nata ya shafe sama da wata uku a hannun ƴan bindigar amma saboda fargabar tsaron lafiyarsa bata nuna ta sanshi ba.

Abubakar Muhammad Dauran, kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar ta Zamfara ya faɗa wa BBC cewa duka mutanen da aka kuɓutar sun fito ne daga ƙaramar hukumar Gwaram a jihar.

A cewarsa, cikin mutanen 10 har da ƙananan yara sai dai ƴan fashin dajin sun sari shi mahifin yarinyar amma "da muka zo da shi an gyara masa kuma yanzu haka dai ita gwamnati idan aka samu irin waɗan nan abubuwan toh za a kai su asibiti domin a kula da lafiyarsu kafin a miƙa su ga iyalansu".

Game da ko an biya kuɗin fansa kafin sakin mutanen kuwa, Dauran ya ce "babu naira ɗaya da aka biya domin abu biyu ne muka ɗauko a jihar Zamfara - muna sulhu da waɗanda suka yadda da sulhu kuma muna yaƙar waɗanda ba su yadda da ainihin sulhu ba".

Kwamishinan tsaron ya ƙara da cewa baya ga mahaifin yarinyar, an kuma kubutar da ƴar'uwarta da ita ma suke tare a wajen ƴan fashin dajin.