You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283299

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Warin bola na korar mutane daga gidajensu a wasu yankuna a Kano

Warin bola na damun wasu mazauna birnin Kano Warin bola na damun wasu mazauna birnin Kano

Wasu mazauna birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya sun koka bisa yadda ake ci gaba da samun yawaitar shara a unguwaninsu da ke cusguna wa rayuwarsu.

Mazauna yankunan da abin ya shafa na wannan koke ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da gudanar da tsaftar muhalli a duk Asabar ɗin ƙarshen kowane wata a jihar.

Wasu daga cikin mazauna jihar na ci gaba da bayyana fargabar irin mawuyacin halin da za su iya shiga a damunar bana, ganin wasu lokutan sai dai su tafi gidan ƴan uwa idan sharar ta dame su.

A unguwar Gama B a yankin karamar hukumar Nasarawa alal misali, dattawan yankin sun ce a mafi yawancin lokuta su kan tsawatar wa yara masu zubar da shara barkatai, ko kuma masu neman ƙarafa ko lalatattun ledoji damin sayarwa.

Akwai wani waje da ake kira unguwar Detsi a Gama B inda sharar da ke wajen ta cika maƙil har ta cika wani wawakeken rami da ake zuba bola a cikinsa, kuma ban da wari babu abin da ke tashi duk da cewa akwai gidaje a kusa da bolar, kamar yadda wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya shaida.

Al'ummar da ke zaune a wannan yanki sun ce warin bolar na cusguna wa rayuwarsu.

Wani mazaanin unguwar Bashir Muhammad Sa'id ya ce: "Muna iya ƙoƙarinmu muna sa masu zubarwa su tura ta cikin rami ko kuma mu sa manjagara da kanmu mu tura ta.

"Wasu lokutan idan warin bolar ya kai iyaka sai dai mu bar layin gaba ɗaya ko kuma mu sanya takunkumi mu rufe fuskokinmu saboda gaskiya abin na jawo gurɓacewar muhalli," a cewarsa.

Ita ma Malama Zakiyya ta ce "gaskiya wannan bola na ba mu matsala sosai musamman ma lokacin sanyi. Idan aka kunna wuta wannan hayaƙin na takura mana kamar mu gudu mu bar layin.

"Idan kuwa aka yi ruwan sama to warin hana mu zama yake gaba ɗaya a layin. Sai dai mu haƙura mu zauna haka, wasu kuma su tafi wani wajen," a cewarta

Ta ƙara da cewa "idan kuwa annobar zazzaɓi ta shiga layin nan to a kan daɗe bai tafi ba."

Wani zagaye da Khalifa Dokaji ya yi a wasu daga cikin unguwanin da ke birnin na Kano, ya ga tulin shara jibge a wasu daga cikin wuraren da aka tanada don zubar da ita, inda mazauna wuraren suka hakura da jiran gwamnati ta kwashe ta.

Amma a cewar gwamnatin Kano, tana sane da yadda ake da dalar shara a jihar, kuma tana daukar mataki a kai, tuni kuma ta shiga wata yarjejeniya da wani kamfani don ɗebe sharar.

Dr. Kabiru Ibrahim Getso shi ne kwamishinan muhalli, ya kuma ce: "Wannan abu ne da ya daɗe ana fama da shi kuma ana jawo hankalinmu a kai. Wato gwamnati ita kaɗai ba za ta iya wannan aiki ba.

"Shi ya sa gwamnati ta sa hannu a wannan yarjejeniya da wani kamfani wanda muna sa ran idan aikin nan ya kankama maganar a zo ana tara shara a cikin unguwannin mutane ta kau.

"An fito da wannan tsari na dauke alhakin kwashe shara daga hukumar kwashe shara ta jihar Kano an bai wa wannan kamfanin.

"Ita kuma hukumar kwashe shara za ta ci gaba da ayyuka kamar feshin maganin ƙwari da sauro da ɓeraye da macizai da kuma wasu ayyuka na musamman da gwamnati za ta fito da su.

"Daya daga cikin abubuwan da muka sa hannu akai shi ne haramta zubar da bola a ko ina barkatai. Dama tuni gwamnati ta samar da gurare da shi wannan kamfani zai zama yana kula da su inda za a dinga zubar da shara," a cewar kwamishinan.

An dauki tsawon lokaci ana kokawa kan yadda ake fama da matsalar zubar da shara barkatai a Kano, wanda a wasu lokutan takan cika magudanan ruwa da ke janyo ambaliya a lokacin damuna.

Haka zalika wannan batu na zuwa ne kasa da mako guda da aka gudanar da Ranar Muhalli Ta Duniya, inda kuma ranar ta bana ta karkata kan yadda za a magance matsalolin shara da ƙarancin bishiyoyi a duniya.