You are here: HomeAfricaBBC2021 09 13Article 1355881

BBC Hausa of Monday, 13 September 2021

Source: www.bbc.com

Waiwaye: Ziyarar da Buhari ya kai Imo da toshe layukan waya a Katsina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Wannan wani tsakure ne daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon jiya.

Yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Borno da Bankin kasashen Larabawa

Gwamnan Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya kulla hulɗar kasuwanci tsakanin Bankin ƙasashen Larabawa kan raya tattalin arzikin Afirka, (BADEA) da ke Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

Yarjejeniyar ta ƙunshi fitar da alkama da ƙaro da manoman Borno ke samarwa.

Jihar Borno ce kan gaba wajen noman alkama da ƙaro a Najeriya.

Gwamna Zulum ya bayyana irin kalubalen da Borno ke fuskanta saboda hare-haren mayaƙan Boko Haram da suka durkusar da tattalin arziki da fannin noma don haka wannan hanya ce da za ta sake farfaɗo da ƙasar.

Rufe makarantu a Jihar Adamawa

Gwamnatin Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta rufe makarantun kwana 30 cikin 34 da ke fadin jihar saboda matsaloli na tsaro.

Sanarwar da kwamishiniyar Lafiya, Mrs Wilbina Jackson ta fitar na cewa an rufe makarantun daga ranar Litinin din da ta gabata har sai baba ta gani.

A cewar sanarwar an ɗauki wannan mataki ne la'akari da taɓarɓarewa lamuran tsaro musamman na ɗalibai a makarantu.

Adamawa na daga cikin jihohohin da ke fuskantar barazana daga hare-haren 'yan bindiga.

Sace ma'aikatan Kamfanin Obasanjo

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikata uku a kamfanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a wani kauye a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Rundunar 'yan sanda ta jihar ta ce a ranar Laraba ce 'yan bindigar suka tare ma'aikatan uku karkashin kamfanin Obasanjo, Obasanjo Holdings da ke Kobape a karamar hukumar Obafemi-Owode

Bayanin Sabo Nanono game da sauke shi da aka yi daga Minista

Tsohon ministan gona na Najeriya Mohammed Sabo Nanono ya ce ba abu ba ne mai sauki rike ma'aikatar gonar kasar ba.

Ya ce ma'aikatu masu zaman kansu na matukar taimakawa wajen mayar da aikin ma'aikatar mai wahala.

Nanono ya bayyana hakan ne yayin mika al'amuran ma'aikatar ga sabon ministan, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, wanda ya gudana a Abuja.

"A wuri na ba abu ba ne mai sauki ba. A matsayina na wanda ya taba aiki a ma'aikata mai zaman kanta, dole a rika samun sabanin muradi a ma'aikatun gwamnati a nan da can. Amma a karshe mun fahimci juna da su."

Kalaman Buhari a Imo

Shugaban Najeriya Muhammad ya ce yana so a rika tunawa da shi a matsayin wanda ya daidaita Najeriya ta fuskar tsaro da tattalin arziki da habbakar kasa da nasarar da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a Owerri ranar Alhamis.

Shugaban ya bayyana wa shugabannin kudu maso gabashin Najeriya a wata ziyara da ya kai ta kwana guda a jihar Imo cewa, cikin abin da ya yi kasa da shekara biyu da ya rage na mulkinsa, har yanzu harkar tsaro ita ce abin da ya fi bai wa mahimmanci.

"Idan babu tsaro, babu wanda ya isa ya yi wani abu, duk yadda za a yi kokarin kawo ci gaba. Tsaro shi ne abu mafi mahimmanci sannan tattalin arziki. Lokacin da mutane ke da cikakkiyar nutsuwa kan harkar tsaro ko wa zai mayar da hankali kan abin da yake gabansa",in ji Buhari.

Toshe layukan salula a Katsina

An toshe layukan sadarwa a wasu sassa na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, kusan mako guda kenan bayan toshe na jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.

Mai bai wa gwamnan Katsina shawara a kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmed Katsina ne ya tabbatar wa BBC da batun katse layukan inda ya ce an ɗauki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.

Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Funtua da Bakori da Jibiya da Malumfashi da Faskari da Batsari da Ɗanmusa.

Sauran kuwa su ne Sabuwa da Kankara da Dutsinma da Kurfi da Safana da Ɗandume.

A cewar Ibrahim Kastina, ya zama wajibi gwamnatin Katsina ta ɗauki wannan mataki, domin hana ƴan bindigar da ke Zamfara gangarawa Katsina su ci gaba da amfani da waya da gudanar da harkokinsu.

Kama wani babban kwamandan Boko Haram da Sojojin Najeriya suka yi

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wani babban kwamandan Boko Haram da ake kira Yawi Modu, wanda a kwanan nan ta ce tana nema ruwa a jallo.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a Abuja jaridar da Premium times ta wallafa, Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ya ce rundunar ta kai wani samame ne wani wurin hada abubuwan fashewa da ke jihohin Yobe da Borno.

Rundunar ta ayyana wasu mutane sama da 100 shekara biyar baya da take nema ruwa a jallo.

Kuma ta wallafa sunayensu tare da makalesu a bainar jama'a.

Wannan na zuwa ne dai a lokacin da wasu mambobin kungiyar ke ci gaba da tuba tare da mika wuya ga jami'an tsaro tare da iyalansu.