You are here: HomeAfricaBBC2021 04 12Article 1230886

BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Waiwaye: Hare-hare a kudancin Najeriya da yajin aikin kungiyoyin kwadago

Gwamnan Sokoto Tambuwal (hagu) tare da tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso Gwamnan Sokoto Tambuwal (hagu) tare da tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 04 ga Afirilu zuwa Asabar 10 ga Afirilu.

Sai dai makon ya fara ne da hutun ranar Easter da kirista a fadin duniya ke bikinta domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.

Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa wayewar garin Juma'a a kuma a kammala a ranar Litinin ta gaba a ko wacce shekara.

Harin da 'yan IPOB suka kai jihar Imo

A farkon makon nan ne aka tashi da wani mummunan hari da ya girgiza kudancin Najeriya da kasar baki daya.

Hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ta ce 'yan bindiga sun kubutar da fursunoni 1,844 daga gidan yarin birnin Owerri na jihar Imo.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Francis Enobore ya fitar ranar Litinin.

Hukumar ta fitar da sanarwar ce a yayin da rundunar 'yan sandan kasar ta dora alhakin kai hari kan hedikwatarta da kuma gidan yarin birnin Owerri kan 'yan kungiyar IPOB ranar ta Litinin da asubahi.

A gefe daya kuma, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce binciken farko-farko da ta gudanar ya nuna cewa 'yan bindigar da suka kai harin mambobin ƙungiyar IPOB ne masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra.

Naɗin sabon shugaban ƴan sandan Najeriya

A dai cikin makon ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan Sandan kasar.

Sabon sufeton zai maye gurbin Muhammad Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.

Kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC hakan.

Usman Alkali wanda aka haifa ranar 1 ga watan Maris na 1963, ya fito ne daga Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Zargin cewa Atiku Abubakar ba ɗan Najeriya ba ne

Ministan Shari'a na Najeriya ya musanta wasu rahotanni da kafafen watsa labarai suka bayar cewa ya fada wa wata kotu cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar bai cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasar ba, don ba haifaffen Najeriya ba ne.

Abubakar Malami ya ce shari'ar da ake magana a kai wata ƙungiya ce mai suna "Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa" (EMA) ce ta shigar da ita tun a shekara ta 2019 kuma shi ma yana cikin wadanda ake ƙara.

Ministan ya yi martanin ne bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi sakamakon labarin da wasu jaridun Najeriya suka wallafa cewa Abubakar Malami ya ce Atiku Abubakar bai cancanci takarar shugabancin Najeriya ba saboda lokacin da aka haife shi garinsu na ƙarƙashin Jamhuriyar Kamaru.

Yajin aikin kungiyoyin kwadago

Manyan kungiyoyin kwadago hudu ne suka tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a Najeriya, lamarin da ya jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.

Wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyar likitoci masu neman kwarewa; kungiyar ma'aikatan kotu; kungiyar ma'aikatan kwalejojin fasaha da kuma kungiyar ma'aikatan majalisun dokokin jihohi.

Masu sharhi sun yi ta sukar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari game da halin ko in kula da ya nuna kan yajin aikin, in da ya yi tafiyarsa Landan neman magani.

Sai dai kuma a cikin makon 'yan majalisun Najeriya sun roki kungiyar likitoci masu neman kwarewa da su koma bakin aiki, rokon da bai samu karbuwa ba.

Yawaitar makamai a Najeriya da tsohon shugaban kasar Abdulsalami Abubakar ya yi magana a kai

Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ya alakanta karuwar tashe-tashen hankula a kasar da yawaitar makamai da aka samu a hannun ɗai-ɗaikun mutane, inda ya ce akwai a ƙalla makamai miliyan shida da ke yawo a hannun mutane ba bisa ƙa'ida ba.

Abdulsalami wanda kuma shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da ya gudana a ranar Laraba a Abuja.

A cewarsa, bazuwar makaman wanda ya haifar da matsalar tsaro a Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 80,000.

Ya ce, "Bazuwar muggan makamai a baki ɗayan Najeriya abin damuwa ne. An yi ƙiyasin cewa akwai fiye da makamai miliyan shida da suka yaɗu a ƙasar nan.

"Wannan rikici na matsalar tsaro ya hallaka mutum 80,000 sannan ta raba kusan wasu miliyan uku da muhallansu," in ji Abdulsalami.

Nasarar kashe yan bindiga 24 da sojin Najeriya suka yi

Akalla 'yan bindiga 24 sojojin Najeriya suka kashe a wani harin sama da suka kai a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna a arewacin kasar.

Karamar hukumar daya ce daga inda 'yan bindigar ke cin karensu babu babbaka a jihar ta Kaduna, an sace mutane da dama an kuma raba da yawa da muhallansu a cikinta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin kwamishinan cikin gida da harkokin tsaro na jihar Samuel Auwan, ya ce an kai harin ne ta sama tare da kashe wadannan bata gari a wata unguwa da ake kira Nacibi da ke karamar hukumar birnin gwari.

Aruwan yace jiragen saman da suka kai harin sun kai ne a inda nan ne maboyar 'yan bindigar, yana mai cewa kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Rufe makarantu da aka yi a Abia saboda matsalar tsaro

Gwamnatin jihar Abia da ke kudancin Najeriya ta ce an gano wani abu da ake tsammanin 'bam' ne a cikin aji a wata makarantar firaimari a Afaraukwu da ke karamar hukumar Umuahia ta arewa.

Kwamishinan yada labarai na jihar, John Kalu ya ce an rufe duka makarantun jihar domin kare rayuwar yara kanana.

Hare-hare dai a yankin Kudu maso gabashin Najeriya na kara kamari, kuma mafi yawansu ana kai su ne kan jami'an tsaro.

Kashe sojojin Najeriya 11 da aka yi a Benue

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Muhammad Yerima ya aike wa manema labarai, ta ce sojoji goma da jami'in tsaro daya ne suka mutu, wadanda a baya ake nema sakamakon ɓatan da suka yi, har aka aike da tawagar hadin gwiwa domin nemo su.

Sai dai tawagar ta samu gawar sojojin a karamar hukumar Konshisha da ke jihar Benue.

Sai dai rundunar sojin ba ta bayyana wani abu game da waɗanda ake zargi da kisan sojojin ko wani abu da ya yi silar ajalinsu nasu ba.

"A yayin da aka yi gaggawar kwashe gawarwakin, ana kuma kokarin gano wadanda suka aikata mummunan aikin domin hukunta su," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa: "Sojojin Najeriyar karkashin jagorancin Laftanal Janar Ibrahim Attahiru na ci gaba da kokarin ganin zaman lafiya ya inganta, da kawo karshen bata gari a kasar baki daya."

Rikicin Kwankwanso da Tambuwal na PDP

Alamu na nuna wata baraka ta kunno kai a reshen jam'iyyar PDP na arewa maso yammacin Najeriya, inda daya daga cikin iyayen jam'iyyar a yankin Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan cikin al'amuran jam'iyyar a jihar Kano.

A cewar Kwankwaso wanda yake jagorantar bangaren Kwankwasiyya ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu ƴaƴan jam'iyyar na Kano da ke hamayya da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na yankin Arewa maso Yamma.

"Abin takaici shi ne akwai shi gwamna na Sokoto, wanda a ra'ayinsa bai kamata mu musamman yan Kwankwasiyya a ba mu wadannan mukamai ba,"in ji Kwankwaso.

To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya musanta wannan zargin inda ya ce "duk wanda yake da sha'awa ya fito ya yi takara."