You are here: HomeAfricaBBC2021 05 11Article 1257925

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Wael al-Saad Tawadros: Ƙibɗiyyin da aka rataye bisa kisan malamin coci a Masar

An gano Bishop Epiphanius kwance cikin jini a watan Yulin 2018 a cocin Saint Macarius An gano Bishop Epiphanius kwance cikin jini a watan Yulin 2018 a cocin Saint Macarius

An rataye wani malamin coci ƙibɗiyyi da aka yanke wa hukunci bisa kisan wani shugaban wata tsohuwar coci a Masar.

An gano Bishop Epiphanius kwance cikin jini a watan Yulin 2018 a cocin Saint Macarius a yankin Western Desert.

Haka kuma, an yanke wa wani malamin cocin hukuncin ɗaurin rai-da rai saboda rawar da ya taka a kisan.

Kisan dai ya jefa al'ummar ƙibɗawa a Masar cikin tashin hankali, wadda ita ce al'ummar kirista tsiraru mafi girma a Gabas ta Tsakiya.

Ana tunanin malaman cocin, Wael al-Saad Tawadros da Remon Rasmi Mansour, sun kashe shugaban cocin ne a filin Wadi al-Natrun da ke arewa maso yammacin Masar saboda wani saɓani da ba a bayyana ba.

An rataye Wael al-Saad Tawadros ne ranar Lahadi - wanda masu shigar da ƙara suka ce ya amsa laifin kwaɗa wa malamin cocin sandar ƙarfe a kai har ya mutu yayin da sauran malaman cocin ke tsaye suna kallo.

Da farko shi ma Mansour an yanke masa hukuncin kisa, amma daga baya ya ɗaukaka ƙara aka rage hukuncin zuwa ɗaurin rai da rai.

Cocin ƙibɗawa ta daina naɗa sabbin malaman coci tsawon shekara guda a wani ɓangare na ɗaukar matakan da aka ɗauka bayan kisan.

Su waye Kiristociƙibɗawa?

Cocin Ƙibɗawa shi ne babban cocin Kirista a Egypt. Yayin da mafi yawan ƙibɗawa ke rayuwa a nan, cocin na da kusan mabiya miliyan ɗaya a wajen ƙasar.

Ƙibɗawa sun yi imanin cewa addininsu ya samo asali ne tun shekara 50 bayan mutuwar Annabi Isa.

Ana kiran shugaban coci Fafaroma, kuma ana ganinsa a matsayin magajin Saint Mark. Fafaroma na yanzu shi ne Tawadros II.

Cocin Ƙibɗawa ya ware kansa daga sauran rarrabe-rarraben Kirista a Taron Majalisar Chalcedon a shekarar 451, a wani rikici akiɗa da ta shafi Yesu Almasihu.

An yi ƙiyasin Ƙibɗawa su ne kashi 10 zuwa 15 cikin ɗari na al'ummar masar miliyan 100.