You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283272

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Twitter: Shin za a iya kama duk wanda ya yi amfani da shafin a Najeriya?

Najeriya ta hana shafin sada zumunta a kasar tun Juni 4 Najeriya ta hana shafin sada zumunta a kasar tun Juni 4

'Yan Najeriya da dama na ci gaba da mu'amala da shafin Twitter bayan da suka kauce wa barazanar da gwamnati ta yi na cafke tare da gurfanar da duk wanda aka kama da karya dokar hana amfani da shafin na Twitter.

Suna amfani da manhajar da ke ba da damar shiga intanet ba tare da shamaki ba ta (VPNs) wajen kauce wa haramcin bayan da kamfanonin sadarwa suka bi umarnin gwamnati na toshe shafin.

Gbenga Sesan na kamfanin Paradigm Initiative, wanda ke bai wa matasa damar amfani da fasahar zamani a fadin Afirka, ya ce reshe ya juye da mujiya kan haramcin na gwamnati.

"Ko kun san me? Da alamu mutanen da aka haramta wa a halin yanzu jami'an gwamnati ne da kansu, kwarai kuwa, wasu kamfanoni sun daina amfani da shafin ne saboda a bayyane take ba sa son a hukunta su, amma kuma 'yan kasar da ake kokarin haramta wa har yanzu suna amfani da shafin,'' ya shaida wa BBC.

A ranar Juma'a ne aka sanar da haramcin bayan da gwamnati ta yi zargin cewa ana amfani da shafin na Twitter wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa ''tashe-tashen hankula''.

Hakan ya haifar da martani mai zafi daga 'yan Najeriya da dama da suke kallon matakin a matsayin taka hakkin bila dama, amma kuma gwamnati ba ta nuna wata damuwa ba, inda ta bar shafin na Twitter a kasar ya ci gaba da kasancewa a toshe.

Ashe za a iya cafke mutum a kan yin amfani da shafin Twitter a Najeriya?

Wasu masana harkokin shari'a sun ce ba su san da wata doka wacce ta tanadi haramci kan amfani da shafin Twitter ba, amma kuma, wasu sun bayyana cewa 'yan sanda za su iya kama duk wadanda ake zargi da karya doka saboda karfin ikon da aka ba su a karkashi dokar da ta shafi tsaron kasa.

Sanannen abu ne cewa jami'an tsaro a Najeriya kan aiwatar da doka ko da kuwa babu tabbaci game da tanadin dokar a kan hakan.

A nasa bangaren, ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya bayyana cewa mutane za su fahimci irin laifin da suka aikata ne kawai bayan a gurfanar da su a gaban kotu.

Gwamnati ba ta yi bayani game da batun cafke kowa ba, amma kuma akwai wasu rahotanni da ba a tabbatar ba da ke nuna cewa ana tsayar da mutane tare da duba wayoyin salularsu a wasu sassan Najeriyar don ganin ko akwai manhajar Twitter a kai.

Galibi dai, shafin na Twitter shi ne babban dandalin da aka fi samun labarai da dumu-duminsu, da kuma neman goyon baya mutane game da matakan jami'an tsaro.

Yanzu akwai fargabar cewa za a iya cafke mutane a tsare su ba tare da wani ya sani ba. Karin wata damuwar kuma al'amuran kotunan kasar sun tsaya cik saboda yajin aikin da ma'aikatansu ke yi, don haka mutane za su ci gaba da zama a caji ofis na 'yan sanda har na tsawon lokaci.

Yajin aikin ya kuma haifar wa da kungiyar lauyoyi ta kasar cikas na zuwa kotu don neman a janye haramcin.

Kungiyar ta bayyana haramcin a matsayin wanda ba shi da hurumi a bangaren doka, kuma ya keta dokar 'yancin 'yan Najeriyar na fadin albarkacin baki.

Shin manyan fitattun mutane na karya wannan dokar haramci?

Kwarai kuwa, musamman ma 'yan adawa - kamar su gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, wanda dan jam'iyar PDP ne, kuma ya kasance mai cike da sukar lamirin gwamnati kan haramta amfani da shafin.

Amma kuma, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, wanda na hannun daman shugaba Buhari ne ya yi amfani da shafin na Twitter.

Manyan jaridun Najeriya kamar su Punch, da Daily Trust da Guardian, wadanda duk suna da shafukansu na intanet sun cigaba da amfani da shafin na Twitter.

Wannan da alamu saboda ba a Najeriya ake lura da shafin yanar gizon ba don haka kamfanonin buga jaridun ba su da wata hukumar da ke sa ido a kan su.

Amma tashoshin talabijin da rediyo suna da hukumar da ke sa ido a kan su wato NBC wacce ta gargade su cewa kauce wa bin dokar na kin goge shafinsu na Twitter zai yi nuni da cewa sun aikata laifin rashin nuna kishin kasa.

NBC din ta kuma ce kada manema labarai su yi amfani da Twitter din wajen tattara bayanai.

Wasu manyan gidajen radio kamar su

Radio Now FM da ke birnin Lagos da Daar Communications sun bi dokar, amma kuma sun ce za u kalubalance ta.

Har ila yau dokar ta shafi kafar yada labarai ta BBC wacce ke da dimbin mabiya a Najeriyar.

"Ma'aikatan na BBC a Najeiya na cigaba da yin mu'amala da mabiyan ta a kan shafin na Twitter da labaran da ake wallafawa ta shafukan BBC Africa da BBC World na Twitter," in ji helkwatar wacce ke Birtaniya a wata sanarwa.

Manyan limaman coci-coci kamar su Redeemed Christian Church of God da Deeper Life Bible Church - su ma suna amfani da shafin na Twitter, duk da cewa babu tabbaci kan ko sun yi daga Najeriya ne ko kuma daga waje.

"Cocin Redeemed Christian Church of God na da rassa fiye da kasashe da yankuna 170. Duk abinda muka walafa a nan yana cikin sashe na 19 na kundin dokar bai-daya Majalisar Dinkin Duniya ta 'yancin biladama ta bai-daya," jaoran cocin Pastor Enoch Adeboye ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin.

Lokacin da BBC ta tambayi Ministan Yada Labarai na Najeriya La Mohammed kan ko za a gurfanar da limaman cocin kan karya dokar ya bayyana cewa:" Ministan shari'a ya fito karara ya bayyana cewa duk wanda ya karya dokar za a hukunta shi. Ministan shari'ar shi yake da hurumin yanke shawara a kan wane ne za a gurfanar ko kuma akasin haka.'

Amma a bangaren kamfanoni masu zaman kan su a Najeriyar akasarinsu - da suka hada da bankuna - sun daina amfani da shafin na Twitter.

Quickteller, wani dandadlin harkokin biyan kudade ta shafin intanet, ya aike da sakon imel wa masu mu'amala da shi cewa zai rufe shafinsa na Twitter na wucin gadi inda ya ba su zabin komawa yin amfani da sauran safukan sada zumunta.

Wane irin tasiri ne dokar haramcin ta yi?

Shafin NetBlocks, mai sa ido kan shafukan intanet na duniya, ya ce Najeriya na tafka asarar kusan dala 250,000 ($250,000) kwatankwacin fan 176,000 (£176,000) a ko wace sa'a daya tun bayan haramta amfani da shafin, kana masu sharhi sun bayyana cewa haka zai cigaba wajen raunana tattalin arziki tare da kara matsalar rashin aikin yi ga matasa.

Shafin Twitter na da taomashi ga akasarin 'yan Najeriya, ana yin amani da dandalin wajen tara kudaden tallafi ga marasa lafiya, da neman motocin daukar marasa lafiya, da taimakawa wajen gano wadanda suka bata, kana ya kasancewa wata hanya ta samun kudaden shiga ga matasan kasar da dama.

Yana kuma da karfin saurin hada kawunan jama'a, inda masu fafutika suka rika yin amfani da shi wajen neman goyon baya a lokacin zanga-zangar neman lawo karshen cin zalin 'yanzanda #EndSars, da ta ja hankulan kasashen duniya kana ta samu goyon bayan taurari kamar su Rihanna, da Kanye West da dan damben boxing Anthony Joshua.

Me yasa aka kafa dokar haramcin?

Wadancan jerin zanga-zangar ta #EndSARS ko shakka babu sun haifar da rashin jin dadi ga Najeriya game da Twitter.

Shugaban kamfanin na Twitter Jack Dorsey ya bayar da gudumawa da daya daga cikin kungiyoyi masu shirya zanga-zangar da kirkiro wasu alamu na musamman saboda zanga-zangar ta yadu a shafukan sada zuunta.

Gwamnati ta kuma zargi kamfanin na Twitter da taimaka wa kungiyar nan mai neman ballewa daga Najeriya da ke fafutikar kafa kasar Biafra a kusu maso gabashin Najeriya.

A makon jiya ne shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter game da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kudu maso gabashin kasar. Ya kuma danganta hakan da yakin basasar shekarar1967 suwa 1970 kana da batun cewa wadanda ke tayar da zaune tsaye, "za a mayar musu da irin harshen da za su fahimta."

Bayan da shugaban ya fuskanci mayar da martani kan kalaman da ya wallafa ne daga masu amfani da shafin na Twitter, shafin ya goge tare da zargin shugaban kasar da karya dokokinta.

Gwamnatin ta fusata inda ta zargi kamfain na Twitter da nuna son kai wajen nuna halin ko in kula ga irin kalaman da Nnamdi Kanu jagoran 'yan aware na kungiyar neman kafa kasar Biafra (IPOB) wanda ke zaman gudun hijira ke wallafawa, ta ta ce ya haifar da kashe-kashen jami'an 'yansanda.

Tuni dai aka goge irin wadannan kalamai da aka wallafa.

Duka bangarorin biyu sun ce suna kan tattaunawa game da takaddamar a wani abu da za a iya cewa kasar ita ce babbar kasuwar Twitter din a Afirka.