You are here: HomeAfricaBBC2021 07 21Article 1314472

BBC Hausa of Wednesday, 21 July 2021

Source: www.bbc.com

Tsoffin 'yan Real da na Barca za su buga El Clasico

El Clasico na tsohon 'yan wasan Barcelona da Madrid zai faru a Isra'ila El Clasico na tsohon 'yan wasan Barcelona da Madrid zai faru a Isra'ila

Tsoffin 'yan wasan Real Madrid da na Barcelona za su buga El Clasico ranar Talata a Tel Aviv, Isra'ila.

Ranar Litinin suka gana da 'yan jarida, inda 'yan wasan suka yi wa dan kwallon Brazil, Ronaldinho tarbar gima, cikinsu har da Deco da Luis Figo da Iker Casillas da kuma Roberto Carlos.

Sauran fitattun tsoffin 'yan kwallon da za su buga karawar sun hada da Rivaldo da Gaizka Mendieta da Jose Amavisca da kuma Juan Pablo Sorin.

An tsara cewar 'yan wasan da suka yi wa kungiyoyin biyu wasa wato Luis Figo da Luis Milla da Alfonso Perez da Javier Saviola da Miguel Soler da kuma Dani Garcia, za su buga wa Real daga baya su yi wa Barca kwallo a karawar.

Tsohon golan Real Madrid, Iker Casillas shine babban bako a matakinsa na jakadan Real Madrid, bayan da ya yi ritaya daga taka leda shekara biyu da ta wuce.