You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283284

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Taron G7: Mene ne taron, kuma me ya sa ake yin sa a Cornwall?

Firaministan Ingila Boris Johnson Firaministan Ingila Boris Johnson

Shugabannin kasashen duniya ciki har da na Amurka Joe Biden da shugabar Jamus Angela Merkel, za su yi wata ganawa a London ranar Juma'a 11 ga watan Yuni.

Taron na kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki da ake kira G7 a takaice, zai kasance ido da ido.

Mene ne G7?

Kungiyar ta G7 dai ta kunshi manyan kasashe 7 na duniya da suka fi karfin tattalin arziki, da suka hada da Canada, da Faransa, da Jamus da Italiya da Birtaniya da Amurka da kuma Japan.

Rasha ta sake shiga kungiyar a shekarar 1998, abin da ya sa ta zama G8, sai dai daga bisani an sake cire ta a shekarar 2015, saboda kwace iko da yankin Crimea.

Ƙasar China ba ta taba kasancewa mamba a kungiyar ba, duk da karfin tattalin arzikinta, da kuma yawan jama'ar da ubangiji ya huwace mata.

Kasashen na da ra'ayin cewa arzikin daidaikun 'yan kasar bai kai yadda za a kira ta a matsayin wadda ta dace ta shiga sahunsu don hada kafada da kafada ba.

Akwai wakilan kungiyar Tarayyar Turai da ke halarta taro, baya ga kasashen Indiya, da Koriya ta kudu da Australia, wadanda dukkansu aka gayyace su a bana

Me ya sa za a yi taron a Cornwall?

Kasar Birtaniya ce ke rike da shugabancin kungiyar G7 a shekarar 2021 kuma ta sanar a watan Janairu cewa taron zai gudana a Otal din Carbis Bay.

Ana ganin yankin a matsayin tsakiyar cibiyar fasahar kere-kere ta Birtaniya. Nuna alamun kere-keren kuma na da muhimmanci ga gwamnati gabanin taron sauyin yanayi na COP26 a Glasgow a watan Nuwamba.

Ba wannan ba ne karon farko da shugabannin duniya ke haduwa a gabar teku. Taron G7 na ƙarshe a cikin 2019 an gudanar da shi a garin Biarritz da ke gabar tekun Faransa.

To sai dai taron zai shafi rayuwar yau da kullun ga mazauna garin da masu yawon bude ido a cikin Cornwall, saboda za a rufe hanyoyi don tabbatar da tsaro.

Gwamnatin Burtaniya ta ce yana da mahimmanci shugabannin duniya su hadu da kansu kuma za a yi gwajin korona a kai a kai.

Me G7 ke yi?

A cikin shekara guda ministoci da jami'ai daga ƙasashe membobin kungiyar na yin tarurruka, da kulla yarjejeniyoyi da buga bayanan haɗin gwiwa kan al'amuran duniya.

Ministocin kudi na kasashen sun yi taro a London, don tattaunawa kan yiwuwar sanya haraji kan manyan kamfanonin fasahar zamani da kuma daukar mataki kan canjin yanayi.

Babban taron shi ne taron shekara-shekara inda shugabannin kasashen ke zama don tattaunawa game da manyan batutuwa a ranar.

An soke taron na shekarar da ta gabata, wanda ya kamata Shugaba Donald Trump ya jagoranta saboda annobar korona.

Shekarar ce kuma ta zamo shekara ta farko da ba a gudanar da irin wannan taro ba tun bayan kafa kungiyar da aka yi a shekarar 1975.

Me zai faru a taron kolin na bana?

Babban batun da tattaunawar za ta mayar da hankali a kai dai shi ne duba yadda za a farfado da harkokin da annobar korona ta durkusar, kamar bangaren lafiya da kuma kare aukuwar wata annoba a nan gaba.

Har ila yau ajandar ta kunshi matsalar canjin yanayi da kasuwanci.

Shugabannin za su isa Landan ranar Juma'a 11 ga Yuni kuma tarurruka za su fara washegari, tare da ƙasashen baƙi waɗanda za su zo a wannan yammacin.

Yawancin tattaunawar dai ana yinta ne cikin sirri, amma akwai lokutan da ake yi a bayyana a gaban yan jarida, baya ga daukar hoto da shugabannin ke yia tare.

A karshen taron, Burtaniya a matsayinta na kasar da za ta karbi bakuncin za ta wallafa wata takardar sanarwar hadin guiwa, wannan ce ke nuna abin da shugabannin suka yi yarjejeniya a kai.

Ana sa ran Firaiministan Birtaniya Boris Johnson zai yi wani taron manema labarai a ranar Lahadi.

Shin za a yi zanga-zanga ?

Zanga-zanga a wannan lokacin abu ne mai wahala, saboda sauye sauyen da aka kawo sakamakon zuwan annobar korona.

'Yan sanda sun yi hayar jirgin ruwan yawo don taimaka wa jami'an yan sandan wajen fiye da 5,000 da za su yi aikin bayar da kariya a wajen.

An gaya wa masu zanga-zangar cewa za su iya taruwa a wuraren da aka amince da zanga-zangar guda hudu, ciki har da daya a Exeter sama da mil 100 daga inda ake taron.

'Yan sanda sun ce "ba za su yi kwance da sirdi, bisa tunanin cewa duk wata zanga-zanga za ta gudana ne kawai a wadannan wurare hudu ba".

Kungiyar masu rajin kare muhalli ta ce tana sa ran mutane 1,000 a zanga-zangar da za su yi a Cornwal.

Shin G7 na da wani iko?

Ba za ta iya fitar da kowace doka ba saboda ta ƙunshi ƙasashe daban-daban tare da tsarin dimokiradiyya na kansu.

Sannan wasu matakan na iya shafar duniya ne baki daya.

Misali, kungiyar G7 ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa asusun duniya don yaki da zazzabin cizon sauro da Cutar Aids a 2002.

An sha caccakar G7 din da cewa tsare tsarenta basu dace da zamani ba, musamman rashin sanya China da Indiya da suka fi yawan jama'a a duniya a cikinta.

Ko a shekarar 2020 sai da shugaban Amurka Donald Trump ya kira ƙungiyar a matsayin wadda ta tara 'yar gargajiya' a cikinta.