You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283293

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

TB Joshua: Waiwaye kan rayuwar ɗan Najeriyar da ya zama fitaccen mai wa'azin Kiristoci a duniya

Fitaccen faston Najeriya TB Joshua ya mutu Fitaccen faston Najeriya TB Joshua ya mutu

Fitaccen malamin addinin Kirista na Najeriya, TB Joshua, wanda ya mutu yana da shekara 57, an ɗauke shi a matsayin mai fada a ji a tsakanin manyan masu wa'azin Kiristoci a talabijin wanda ya yi gwagwarmaya don samun karɓuwa daga sauran malaman kiristoci har zuwa mutuwarsa, duk da yana da miliyoyin mabiya a faɗin Afirka.

Baya cikin ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da kuma ta PFN wanda suka bayyana a matsayin wani "mayaudari" ɗan ƙungiyar "asiri" da suka yi kutse cikin addinin Kiristanci.

Amma Mista Joshua ba shi da bambanci da sauran masu wa'azin Kirista na talabijin da suke da'awa tun farkon shekarun 1990.

Yawancin wa'azinsu na tattare da abubuwan ban mamaki da ƙoƙarin nuna "mu'ujiza" kamar Mista Joshua da ba ya cikinsu wanda jagorantar cocinsa ta SCOAN.

"Ba shi da natsuwa, kuma tsarin da yake bi ya saɓa," in ji Abimbola Adelakun, a sashen nazarin Afirka a Jami'ar Texas.

'Suna tunanin jabun fasto ne'

Mista Joshua ya fito ne daga gidan marasa karfi kuma ya girma ne ƙarƙashin kawunsa wanda Musulmi ne bayan rasuwar mahaifinsa kirista.

Ya fi sanya jallabiya - doguwar rigar da yawanci Musulmi suke saka wa, kuma ya bar gemu wanda ya ba shi wata siffa ta daban.

Lokacin da Mista Joshua ya fara wa'azinsa a talabijin a tsakiyar 1990, gashinsa ba ya ƙyalli, haka ma takalminsa kuma akwai tasirin harshen Yarbanci a maganarsa, da kuma Ingilishi da Turancin buroka.

Mabiyansa na masa kallon mai kwarjini, kuma sakonsa ya yadu a duniya.

Mista Joshua ya gyara kansa yayin da ya zama attajiri, inda yake da motocin ƙasaita da jirgin sama na ƙashin kansa, amma kuma yana nan a matsayin baƙo.

Yawancin malaman kirista sun biyo tsari ne bin aƙida inda ake ɗaukar manyan fasto-fasto a matsayin "baba da mama a gun Ubangiji."

"Ba su imani da cewa mutum zai iya zama uban gidan kansa ba tare da ko dogara da wani ba," in ji Gbenga Osinaike mawallafin jaridar Pentecostal ta Najeriya.

"Tsarin na ganin dole kana buƙatar a ce kana bin wata aƙida - Paul, mahaifin Timothy, Elijah, mahaifin Elisha, da sauransu. Suna ganin cewa shi na jabu ne."

Faston, wanda aka haifa 12 ga watan Yunin 1963, Mista Joshua ba ya taimaka wa kansa ba tare da haifar da ruɗani ba - ɗaya daga cikinsu shi ne cewa ya shafe watanni 15 a cikin mahaifiyarsa.

Don sauraren zaman addu'o'insa a farkon wa'azinsa a gidan talabijin wasu da dama na alaƙantawa da ayyukan wata ƙungiyar asiri.

Wasu na ganin kamar wani aikin da ya shafi motsa jiki, wasu kuma na ganin wani matsafi ne ke aiki.

Ba ya zama wani abin mamaki idan yana addu'o'i, kuma da ƙoƙarin ƙarfafa ƙwazo lokacin da yake ikirarin fitar da aljani ko matsala daga jikin mutane.

Amma yana amfani da wani ƙarfi na daban - mutane kan faɗi lokacin da yake yarfa hannayensa, yana birgima yana yarfi da yatsunsa, kuma numfashinsa na komawa a lokacin da yake bin sahun mabiyansa.

Ƙyalle na musamman

Wasu lokuta, yakan kalli wasu daga cikin waɗanda yake yi wa addu'a yana kuma ƙoƙarin kula da motsin saura da wani abin da ba a gani.

"Mutane suna da wani tunani kan yadda Ubangiji zai iya yin komi, kuma idan suka ga wani abu na daban, sai abin ya ba su mamaki," in ji Mista Osinaike.

Amma abubuwa da dama da ake ƙalubalantarsa a lokacin, wasu da dama na aikata irin abin da yake yi.

Suna amfani da farin ƙyalle, suna sayar da mai da ruwa da suke kira masu tsarki da suke ikirarin suna warkar da ko wace irin cuta.

"Amma saboda ba ya cikin ƙungiyoyin, ko yarda da aƙidarsu, ana masa kallon mai aikata saɓo," in ji Mr Osinaike.

Sauran fasto-fasto kamarsa na ƙalubalantarsa da yin wa'azi da nuna karamomi na ƙarya, yayin da kuma yake jaddada cewa na gaskiya ne.

A martaninta, Misis Adelakun ta ce: "babu wata mu'ujiza ta gaskiya."

Na san cewa ba wannan ne ba ne Kiristoci da dama za su amince amma babu wata mu'ujiza da za ta sa kafafunka su miƙe. Babu yadda za a yi a tayar da matacce. Dukkann waɗannan wasu hanyoyi ne na taimaka maka ka yi imani."

Misis Adelakun ta ƙara da cewa wasu kiristocin sun yi imani cewa abubuwan al'ajabi suna ƙare wa a zamanin malaman.

"Amma sai ga zamanin Pentecostals da suke waɗannan abubuwan na al'ajabi na iya faruwa," in ji ta.

Yin amfani da damar dakatarwar talabijin

Manyan fastocin sun sauya fasalin Kiristanci a Najeriya da wa'azi na bishara, abubuwan al'ajabi.

Suna jagorantar taron jama'a kuma yawancinsu ana zarginsu da yin amfani da talakawa kan alƙawuransu na ci gaba.

"Mutane suna son ganin abubuwan ban mamaki. Yana ba su wani abin da za su yi tunani akai," in ji Misis Adelakun.

A 2004, hukumar kula da kafofin yaɗa labaran Najeriya ta haramta kafofin yada labarai yaɗa ayyukan faston a talabijin.

Mista Joshua ya yi amannar cewa dalilinsa ne ya sa aka ɗauki matakin, yayin da fastocin da ke hamayya suka nemi gwamnati da ta tabbatar da haramcin saboda ya mamaye kafafen yaɗa labarai da abin da ya kira mu'ujizarsa.

Ya yi amfani da haramcin zuwa ga ci gabansa, ta hanyar ƙaddamar da tashar talabijin ta tauraron ɗan adam wato Emmanuel TV, wanda ya ƙara faɗaɗa ayyukansa zuwa ƙasashen duniya.

"Shi ne kila na farko da ya fara amfani da intanet da tauraron ɗan adam yana yaɗa wa'azinsa ga mabiya a duniya," in ji Misis Adelakun.

Ya kuma buɗe shafukan Facebook da YouTube wanda ke da miliyoyin mabiya.

A watan Afrilu YouTube ya dakatar da shafinsa saboda wasu saƙwanni na nuna ƙiyayya da luwaɗi.