You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225513

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: bbc.com

Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban ƴan sandan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon mukaddashin babban sufetan 'yan sanda kasar.

Sabon sufeton zai maye gurbin Muhammad Abubakar Adamu wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.

Kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC hakan.