You are here: HomeAfricaBBC2021 09 13Article 1355872

BBC Hausa of Monday, 13 September 2021

Source: www.bbc.com

Romelu Lukaku ya ci kwallon farko a Stamford Bridge

Chelsea ta doke Aston Villa 2-0 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka fafata a Stamford Bridge ranar Asabar.

Romelu Lukaku ne ya fara ci wa Chelsea kwallo minti 15 da fara tamaula, kuma ta farko da ya ci a Stamford Bridge a wasa na 15 a filin.

Mateo Kovacic ne ya ci wa Chelsea na biyu, bayan da suka koma zagaye na biyu da hakan ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.

Lukaku ya koma Chelsea daga Anderlecht a 2011, wadda ta bayar da shi aro ga West Brom a 2013.

Daga nan ta bayar da shi aro ga Everton a 2013, wadda ta mallaki dan kwallon tawagar Belgium a 2014.

A 2017 Everton ta sayar da Lukaku ga Manchester United, ita kuma ta sayar da shi ga Inter Milan, wadda ya lashe Serie A a kakar da ta wuce.

A kuma kakar shekarar nan Chelsea ta sake daukar Lukaku daga Inter Milan a matakin na biyu mafi tsada a Burtaniya, bayan Jack Grealish da Manchester City ta dauka a bana.

Wannan wasan shine na 600 da Chelsea ta ci a Premier League, ita ce ta biyu a wannan bajintar bayan Manchester United.

Haka kuma maki na 48 da Thomas Tuchel ya hada a gasar tun zuwan sa Stamford Bridge cikin watan Janairu, kuma Manchester City ce ta hada 51 a wannan lokacin.

Kuma kwallo 14 ne ya shiga ragar Chelsea tun bayan da tsohon kocin Paris St Germain ya karbi jan ragamar kungiyar ranar 26 ga watan Janairun 2021.

Cikin wasa hudun da Chelsea ta buga da fara Premier League ta bana ta ci uku da tashi 1-1 da ta yi a gidan Liverpool.