You are here: HomeAfricaBBC2021 05 11Article 1258081

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Rikicin Kudus: Muhimmancin masallacin Kudus ga Musulmi, Kiristoci da Yahudawa

Masallacin Kudus na da muhimmanci ga Musulmi, Kiristoci da Yahudawa Masallacin Kudus na da muhimmanci ga Musulmi, Kiristoci da Yahudawa

An shiga ranara ta uku ana arangama tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Palasdinawa a wajen masallacin Al-Aqsa - wurin ibada na uku mafi tsarki ga musulmi da ke birnin Kudus.

Lamarin na faruwa ne a yayin da Yahudawa suke gudanar da tattaki na nuna kishin kasa a birnin Kudus da ke fuskantar tashin hankali a yan makwannin nan.

Sama da mutum 200 ne suka ji rauni sannan jama'a sun rika jefa duwatsu yayin da yan sanda suka rika harba gurneti.

Duk da cewar birnin ne silar daya daga cikin abubuwan da suke jawo tayar da jijiyar wuya tsakanin mabiya addinan Musulunci da Yaduwadanci da Kiristancii, dukkansu sun yi tarayya kan girmama wannan wuri mai tsarki.

Tsohon birnin Kudus yana tsakiyar birnin ne a yanzu inda kwaroro-kwaroro masu yawa da kuma tsarin gine-gine na tarihi sun bambance bangarorin Kiristoci da na Musulmai da na Yahudawa da kuma na Aarmeniyawa.

Tsohon birnin yana kewaye ne da wata ganuwa mai kama ta dutse kuma tana dauke da wasu wurare mafiya tsarki ga al'ummun duniya.

Ko wacce unguwa na wakiltar al'ummarta ne. Kiristoci na da unguwanni biyu saboda Armeniyawa ma Kiristoci ne kuma unguwarsu - wacce ta fi kankanta cikin hudun - daya ce daga cikin tsoffin cibiyoyin Armeniyawa a duniya.

Wani abu ne na daban saboda al'ummar Armeniyawa sun adana al'adarsu cikin Majami'ay St James wadda ta kunshi da yawa daga cikin unguwarsu.


Majami'ar

A cikin unguwar Kiristoci akwai Majami'ar da ake ce wa Church of the Holy Sepulchre a turance, wadda take da muhimmanci ga Kiristoci a fadin duniya. Majami'ar na wani wuri da aka yi imanin cewar yana da alaka da labarin Annabi Isa (AS).

Da yawan Kiristoci sun yi imanin cewar an gicciye Annabi Isa ne a wurin nan tsaunin Golgotha, ko kuma tsaunin Calvary, inda suka yi imanin cewar inda aka binne shi yana wajen da ake ce wa sepulchre din, kuma ta nan ne suka yi imanin cewar ya tashi.

Wakilai daga majami'u daban-daban, ciki har da Cocin Girka da ta darikar Katolika da ta Armeniyawa da ta Kibdawa ne suke gudanar da lamuran cocin.

Majami'ar daya ce daga cikin wuraren ibada ga miliyoyin Kiristoci da ke zuwa bauta inda suka yi imanin cewar an bunne Annabi Isa (AS) domin neman kwanciyar hankali da kuma tabarruki ta addu'a a wurin.


Masallacin

Unguwar Musulmai ita ce unguwa mafi girma daga cikin unguwanni hudu kuma a cikinta akwai Qubbat al-Sakhrah da massalacin Al-aqsa da ke kan wani tudu wanda Musulmi suka fi sani da Haram al-Sharif, ko kuma wuri mai tsarki.

Masallacin shi ne masallaci na uku a tsarki cikin addinin Musulunci kuma yana karkashin gudanarwar wani kwamitin amintattu da ake kira Waqf.

Musulmi sun yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya taho nan daga Makka a daren Isra'i da Mi'iraj kuma ya ja dukkannin Annabawa sallah.

Wasu 'yan taku kadan daga wannan wuri a Qubbat al-Sakhrah akwai wani dutsen da Musulmi suka yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya tashi zuwa sama bayan sallar.

Musulmai su kan ziyarci wannan wuri mai tsarki a ko wane lokaci cikin shekara, amma ko wacce ranar Juma'a a cikin watan Ramadan dubun-dubatar musulmi na zuwa domin su yi sallah a masallacin.


Bangon

A cikin unguwar Yahudawa akwai wata katanga ta yammaci da ake ce wa Kotel, ko kuma katangar yammaci, sauran katangar hana zaizayar tudun da ada wurin ibadan Yahudawa ke zaune.

A cikin wurin ibadar akwai inda ake ce wa Holy of Holies a turance, wato wuri mafi tsarki a addinin Yahudanci.

Yahudawa sun yi imanin cewar nan ne tushen inda aka halicci duniya, kuma inda annabi Ibrahim (AS) ya nemi ya yi hadya da dansa annabi Is'hak (AS). Wasu da dama kuma sun yi imanin cewar inda Qubbat al-Sakhrah yake a yanzu nan ne wuri mafi tsarki a addininsu wanda ake ce wa Holy of Holies.

A yau katangar yammaci ita ce wuri mafi kusa da Yahudawa za su iya ibada ga wuri mafi tsarki a gunsu da ake kira Holy of Holies.

Limamin Yahudawa na katangar yammaci shi yake lura da lamura a wannan wuri, kuma a ko wacce shekara miliyoyin baki na zuwa wurin katangar. Yauhudawa daga fadin duniya sukan ziyarci wannan wuri a lokacin hutun Yahudawa da ake ce wa High Holidays a turance domin yin addu'a da kuma tunawa da tarihinsu.

Rikicin baya-bayan nan

Yan sandan Isra'ila sun ce dubban Palasdinawa sun killace kansu cikin ginin cikin tsammanin yiwuwar samun arangama a lokacin tattakin.

An bai wa yan sandan umarnin shiga cikin masallacin domin tarwatsa masu tayar da hankalin bayan da aka kai wa shingen yan sanda hari sannan jama'a suka rika jefa musu duwatsu.

An shafe sama da sa'a daya yan sanda na harba gurneti kan Falasdinawan da ke jefinsu da duwatsu.

Yan sandan Isra'ila sun yanke shawarar hana Yahudawa zuwa inda masallacin yake a lokacin tattakin.

Bikin da ake yi kowace shekara yana nuna ranar da aka mamaye Gabashin Kudus a 1967 daga baya kuma ya fada hannun Isra'ila a wani mataki da galibin kasashen duniya ba su amince da shi ba.

Kudus ta Gabas ta kasance a cikin 1967 sannan daga baya Isra'ila ta hade ta - a wani matakin da galibin kasashen duniya ba su amince da shi ba.

Falasdinawa na ganin gudanar da bikin wani salon takala ne. Kuma tattakin na zuwa ne yayin da aka shiga ranakun 10 na ƙarshe a watan azumin Ramadana.

Rikicin na baya-bayan nan na zuwa ne bayan shafe kwanaki ana arangama tsakanin Falasdinawa da yan sandan Isra'ila a kusa da yankin Sheikh Jarrah da ke Gabashin Kudus tare da yiwuwar korar Falasdinawa daga gidajensu.

A ranar Litinin ne ya kamata Kotun Kolin Isra'ila ta tattauna kan halin da ake ciki amma aka dage saboda rikicin.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kuma zai gana ranar Litinin domin tattauna batun.