You are here: HomeAfricaBBC2021 04 30Article 1247110

BBC Hausa of Friday, 30 April 2021

Source: BBC

Rikicin Chadi: Dakarun ƙasar da 'yan tawaye sun ci gaba da gwabza faɗa a Lardin Kanem

Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun sojin Chadi da 'yan tawayen FACT Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun sojin Chadi da 'yan tawayen FACT

Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun sojin Chadi da 'yan tawayen Front for Change and Concord (FACT) a lardin Kanem kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI a yankin ya bayyana.

Gidan rediyon ya ce sojin saman kasar Chadi sun yi lugudan wuta ta sama a kan motocin a-kori-kura na kungiyar ta 'yan tawayen FACT yayin da sojin kasa ke kai hari ta kasa bayan kara hada runduna a kusa da garin Mao a lardin Kanem.

Dakarun 'yan tawayen da suka shiga kasar ta Chadi daga kasar Libya a ranar 11 ga watan Afrilu sun yi arangama da sojojin kasar a lardin Kanem a ranar 19 da 20 Afrilu kafin su ja da baya, inda aka bayar da rahoton cewa sun ketara ta kan iyakar yammaci zuwa cikin Jamhuriyar Nijar, bayan da suka suka sha kashi.

A makon jiya ne tsohon shugaban kasar Idris Deby ya mutu sakamakon munanan raunukan da ya samu lokacin fafatawa da 'yan tawaye.

Daga bisani, rundunar sojin kasar ta nada dansa Mahamat Idriss Deby wanda aka fi sani da Janar Kaka domin ya jagoranci kasar tsawon watanni 18.

A farkon mako ne gwamnatin Sojin Rikon Kwarya ta kasar Chadi (CMT) ta yi watsi da tayin sulhu da 'yan tawayen suka yi tana mai cewa a shirye take ta ci gaba da yin gumurzu da su.

Tuni dai sojojin Jamhuriyar Nijar suka fatattaki 'yan tawayen zuwa kasar Chadi.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kasar ta Chadi na kokarin yi wa 'yan tawayen na FACT kawanya da zummuar "halaka" su. Kodayake har yanzu kungiyar ta FACT ba ta ce komai ba.

Gwamnatin Sojin Rikon Kwarya ta kasar Chadi (CMT) ta tabbatar da cewa an kashe akalla mutane shida a lokacin da jami'an tsaro suka tarwatsa 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula da suka yi zanga-zangar 'yan adawa ita a ranar 27 ga watan Afrilu, kamar yadda jaridar Alwihda ta kasar ta wallafa a shafinta na intanet.

Gwamnatin ta mika sakon jaje da ta'aziyyar ta ga iyalan wadanda suka rasa rayukan nasu, amma kuma ta dora alhakin faruwar hakan kan masu zanga-zangar.

Sojojin Chadi na kan gaba a yakin da kasashen Yamma da ma makwabtanta suke yi da masu ikirarin kishin Musulunci a yankin Tafkin Chadi.