You are here: HomeAfricaBBC2021 05 01Article 1248508

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Ramadan: Mabiya wasu addinai da ke jin dadin yin azumin watan Ramadana

Mabiya wasu addinai sun nuna jin dadin yin azumin watan Ramadana Mabiya wasu addinai sun nuna jin dadin yin azumin watan Ramadana

Rehan Jayawickreme, wanda matashin dan siyasa ne a Sri Lanka ya bayar da sanarwar ba-zata a ranar 13 ga watan Afrilu.

"Ni mabiyin addinin Buddah ne kuma ina kokarin bin koyarwa addinina."

"Bayan haka kuma ina shauki kuma na zaku na fara yin azumi tare da yan uwana musulmi maza da mata a lokacin watan Ramadana."

"Wannan ne karon farko da zan gwada yin azumin, saboda haka ina neman addu'arku."

Shi ne shugaban hukumar da ke kula da tsarin birane a garin Weligama da ke kudancin Sri Lanka, kuma tun ranar da aka fara azumin watan Ramadana a 14 ga watan Afrilu bai sake cin abinci ko abin sha ba da tsakar rana.

A wani abu da ba a saba gani ba a Sri Lanka wadda akasarin al'ummarta mabiya addinin Buddah ne, Musulmi sun fara azumin watan Ramadana rana daya da ranar da al'ummar Sinhala da Tamil ke murnar sabuwar shekararsu.

Amma mabiya addinai a Sri Lanka sun kadu kusan shekaru biyu da suka wuce, a lokacin da masu tsattsauran ra'ayi suka kai harin kunar-bakin-wake a wasu majami'u yayin da ake bikin Easter, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 270.

Dan siyasar ya ce ya yanke shawarar yin azumin ne da nufin tunkarar matsalar kudin goro da ake yi wa musulmi saboda hare-haren da masu tsattsauran ra'ayi ke kai wa.

Shafin Twitter na Rehan Jayawickreme ya samu dimbin sakonnin nuna goyon baya, inda kuma wasu ke cewa yin azumin watan Ramadana ga wanda ba musulmi ba ba wani sabon abu ba ne.

Marianne David, wadda yar jarida ce da ke zaune a babban birnin Sri Lanka wato Colombo, ta rubuta cewa ta jima tana yin azumin watan Ramadana.

"Ni mabiya darikar Katolika ce kuma ina azumin watan Ramadana.Yana sa na samu natsuwa, da jinkai, da salama da kuma tarbiyya. Ina maka fatan alheri," a cewarta.

Anuradha K Herath wadda darakta ce kan harkokin kasashen waje a ofishin Firaiminista ta ce ita ma ta taba yin azumin watan Ramadana.

"Ni ma na tuna azumin da na yi a lokacin ina karatu a jami'ar Moratuwa," kamar yadda ta rubuta a shafinta na Twitter.

"Kawata @sifaan ce take tashi na daga bacci idan lokacin sahur ya yi, kuma a raba mana abinci a lokacin da muke lakca don mu bude baki da shi. Za ka ji dadin yin haka gaskiya."

Adawa da nuna wariya"Na yi tunanin yin haka da nufin nuna rashin amincewa da yadda wasu shugabanni ke goyon bayan nuna wariya a kasarmu," a cewar Rehan Jayawickreme. Ba wai na shiga musulunci ba ne, ina adawa ne kawai da nuna wariya."

Ya fada wa BBC cewa an shafa wa mabiya addinin Musulunci a Sri Lanka bakin fenti tun lokacin da aka kai hare-hare yayin bikin Easter.

Kusan kashi 70 na al'ummar Sri Lanka mabiya addinin Buddah ne. Sauran kuma sun kunshi a mabiya addinan Hindu da Musulunci da kuma darikar Katolika.

"A duk lokacin da na nuna wa Musulmi cewa mun damu da su, suna samun nutsuwa su kuma ji cewa ana tare."

Sai dai masu sukar Rehan Jayawickreme na cewa ya yi hakan ne domin kawai ya samu kuri'ar Musulmi.

Amma kuma ya mayar musu da martani ta yin nuni ga ra'ayin wani magoyi bayansa wanda ya rubuta cewa: "Ya fi ka nemi kuri'a ta hanyar hada kan addinai a kan neman kuri'a ta hanyar haifar da kiyayya."

'Ciyar da al'umma'

Yar jarida Marianne David wadda mabiya darikar Katolika ce ta shafe shekaru 15 tana yin azumin watan Ramadana. Ta ce tana amfani da lokacin ta aiwatar da muhimman abubuwa da ke da tasiri a rayuwarta.

"Azumi na sa ka daina tunanin me za ka ci, kuma haka zai sa ka daina ciye-ciye na rashin dalili."

Ta yi imani cewa azumi na sa ta samu kaifin basira kuma yana sa ta samu lafiya.

"Ba wani abu ne mai wahala ba don mutum ya yi azumi, musamman idan ya duba matsayinsa da kuma aikin da yake yi," kamar yadda ta fada wa BBC.

A gare ta babban darasi a watan Ramadana shi ne fahimtar halin da wadanda abinci ke musu wahalar samu a Sri Lanka.

Sadaka na da muhimmanci. Saboda haka yana da kyau a lokacin da kake azumi ka rika sadaka gwargwadon hali, a kuma ciyar da wadanda ba su da zarafi don su samu yin azumin cikin wadata.

Sadaukarwa

A wani bangare na duniya Nadyne Parr daga Amurka ita ma tana cikin wadanda ba musulmi ba da ke azumin watan Ramadana.

Kirista ce da wata kawarta musulma ta fahimtar da ita falalar azumin.

"Na dauke shi a matsayin sadaukarwa ga 'yan uwana Musulmi a matsayina na mai bin addinin Kirista, shi ya sa ma nake yin azumin na watan Ramadana."

Nadyne marubuciya ce, kuma malamar makaranta a jihar Michigan.

"An dauki dogon lokaci ina bin tsari da dokokin azumin watan Ramadana. Nakan karya kumallo da sassafe kuma ba zan sake cin abinci ba har sai rana ta fadi," a cewarta.

"Irin hadin kan da yake kawowa tsakanin addinai da al'adu ne na fi so game da Ramadana."

"A karshe hakan yana nuna mana muhimmancin hada kai a tsakaninmu."

Lokacin hada kai

Idan muka koma Sri Lanka, Marianne David ta fadi cewa "ba wai batun sadaukarwa ba ne da kuma samun nutsuwa, lokaci ne na hadin kai da kuma taya juna murna."

A duk lokacin da muka je bakunta ko kuma muka karbi baki, sai na ji kamar mun shirya cin abinci ne na musamman," a cewarta.

Ta kara da cewa "kuma muna gwada wasu nau'ukan abinci duk da cewa yawan abincin da mutum ke ci yakan ragu idan azumi ya yi nisa.

"Abin da dai nafi kewa shi ne ruwa, musamman a yanayin da ake ciki na zafi. To amma duk da haka amfanin da yin azumin ke da shi ya rinjayi komai."

Ga Nadyne azumi ya zama wani bangare mai muhimmanci a rayuwarta.

Ta yi imani da cewa shafe wani lokaci ba tare da ci ko sha ba yana kara imani.

"Duk lokacin da muka ce abinci za mu rika ci za mu rika rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwa."

Ba sauki

Amma ga Rehan Jayawickreme, wanda sabo ne a harkar ba abu ne mai sauki ba.

"Nakan tashi da karfe hudu na safe na ci dabino da madara da kuma sauran ya'yan itatuwa. Daga nan kuma ba zan sake cin komai ba har sai 6:30 na yamma," kamar yadda ya fada wa BBC.

Amma ya ce duk da haka a karshe azumin yana sa ya wartsake, duk da yana shakkun ko zai iya azumtar Ramadana daga farko zuwa karshe.

"Zan ci gaba da yi matsawar na ji zan iya," a cewar dan siyasar. Sai dai ya ce "abu ne mai matukar wahala a ce ba ka shan ruwa."