You are here: HomeAfricaBBC2021 03 31Article 1220452

BBC Hausa of Wednesday, 31 March 2021

Source: BBC

PDP ta zargi Buhari da nuna halin ko in kula ga halin da 'yan Najeriya ke ciki

Hotunan Uche Secondus (hagu) Chairman na PDP da Shugaba Buhari Hotunan Uche Secondus (hagu) Chairman na PDP da Shugaba Buhari

Babbar Jam`iyyar adawa a Najeriya PDP ta yi zargin cewa tafiyar shugaba Buhari zuwa Ingila don a duba lafiyarsa, alama ce da ke nuna cewa shugaban ƙasar bai damu da halin da ƴan ƙasar ke ciki ba.

PDP ta ce ba daidai ba ne, Shugaba Buhari ya sa ƙafa ya fice daga ƙasar a daidai lokacin da likitoci ke yajin aiki saboda rashin biyan haƙƙoƙinsu da ƙarancin kayan aiki ba. 

Sakataren PDP na ƙasa Sanata Umar Ibrahim Tsauri, ya ce wannan bulaguron na nuna cewa gwamnatin APC ta gaza wajen sauke manyan alƙawurran da ta yi na inganta rayuwar ƴan Nijeriya, ciki har batun kula da lafiyarsu.

''A ƙarƙashin wannan mulki asibitocin Najeriya sun zama kamar wurin zuwa karbar shawara, iyaka kaje a fada maka magani ka je ka siya saboda rashin magungunan a can, ko kwananan nan sai dai aka ce za a yi amfani da kuɗin da aka tara na gudummawar yaƙi da annobar korona don gyara asibitoci, har yanzu wanne asibiti ake gyara ?'' inji PDP.

Sanata Tsauri ya ƙara da cewa ''Idan har da gaske an gyara asibitocin Najeriya, to me yasa shugaba Muhammadu Buhari ya sa kafa ya fice daga kasar maimakon ya tsaya a duba lafiyarsa a nan ?''.

''Yau ɗin nan menene matsayin likitocin Najeriya ?, ai yajin aiki suke yi, amma duk da haka ya bar ƙasar ya tafi neman lafiya a wani waje, to kai a matsayinka na ɗan Najeriya ya zaka kalli wannan abu ?'' inji sakataren na jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Ita dai fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce tafiyar tasa ba wani sabon abu bane, domin dama duk shekara yakan je Ingila don duba lafiyarsa tun ma kafin ya hau kujerar shugaban ƙasa.

Ana sa ran shugaban zai koma gida a mako na biyu na watan Afrilu, sannan shine zai ci gaba da zama a matsayinsa na shugaban ƙasa ba tare da ya mika harkokin mulki ga mataimakinsa ba.

Sai dai jam'iyyar PDP ta ce akwai ayar tambaya game da yadda rana guda aka ji fadar shugaban ƙasar ta fitar da wannan sanarwa ta cewa shugaba Buhari zai je Landan don duba lafiyarsa, amma masu magana da yawunsa sun ce maganar gaskiya ita ce ya ma zarce lokacin da ya kamata ya je, saboda annobar korona.

A shekarar 2017 shugaba Muhammadu Buhari ya shafe fiye da watanni uku yana jinya a Landan, kafin daga bisani ya sake komawa gidan bayan da ya samu lafiya.