You are here: HomeAfricaBBC2021 04 04Article 1224010

BBC Hausa of Sunday, 4 April 2021

Source: bbc.com

Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 28 ga Maris zuwa Asabar 03 ga Afirlu.

Iƙirarin Boko Haram na harbo jirgin sojin Najeriya

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi watsi da wani bidiyo da ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin harbo jirgin rundunar sojin saman a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar ta ƙaryata Boko Haram ne cikin wata sanarwa da kakakinta Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar inda sanarwar ta ce bidiyon ƙarya ne aka haɗa domin yaɗa farfagandar Boko Haram.

Rundunar sojin ta ce tana tunanin jirgin ya yi hatsari ne.

A ranar Laraba ne rundunar sojin saman cikin wata sanarwa ta bayyana bacewar jirgin nata mai kirar Alfa Jet (NAF 475) mai dauke da mutum biyu.

Bidiyon ya nuna mayaƙa ɗauke da makaman harbo jirgin sama da masu cin dogon zango, da kuma tarkace da gawar matuƙin jirgin.

Rundunar sojin ta ce an tsayar da bidiyon aka haɗa yadda jirgin ya kama da wuta daga sama yayin da yake kokarin fadowa.

Rundunar ta sojin saman Najeriya ta ce ko da yake har yanzu tana nazarin bidiyon, amma a bayyane yake cewa yawancin sassan bidiyon an haɗa ne da gangan don yaɗa ƙaryar cewa an harbo jirgin.

Rahoton Amurka kan kisan almajiran Zakzaky

Wani rahoton Amurka kan batun kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya cikin shekara ta 2020 ya ce har yanzu babu wani ƙarin bayani kan binciken gwamnatin tarayya ko kama wasu da hannu a kashe-kashen da sojojin ƙasar suka yi wa ƴan Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Amurka ta ce kamata ya yi a ce zuwa yanzu Najeriya na da wani ƙarin bayani da za ta iya yi wa duniya a kan zargin da ake yi wa dakarun sojin ƙasar na kisan almajiran Zakzaky kimanin 347, da kuma binne su a manyan kaburbura domin boye abin da aka aikata.

Rahoton ya kuma yi dogon sharhi kan take haƙƙin ɗan adam a shekara ta 2020, kama daga kan wanda ake samu a tsakanin jami'an tsaron kasar da kuma kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya.

A wasu bangarorin kuma ya kalli ci gaban da aka samu kan kokarin kare hakkin dan adam, ciki har da hukuncin shekara 55 a gidan maza da aka yanke wa wani soja a watan Agusta, bayan kotun soji ta same shi da laifin aikata kisan kai a jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin kasar.

Tafiyar Buhari Landan

A makon da ya gabata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi Landan domin ganin likitansa.

Tafiyarsa ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman daga ɓangaren masu adawa.

Babbar Jam`iyyar adawa a Najeriya PDP ta yi zargin cewa tafiyar shugaba Buhari zuwa Ingila don a duba lafiyarsa, alama ce da ke nuna cewa bai damu da halin da ƴan ƙasar ke ciki ba.

PDP ta ce ba daidai ba ne, Shugaba Buhari ya sa ƙafa ya fice daga ƙasar a dai-dai lokacin da likitoci ke yajin aiki saboda rashin biyan haƙƙoƙinsu da ƙarancin kayan aiki.

Fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce tafiyar tasa ba wani sabon abu bane, domin dama duk shekara yakan je Ingila don duba lafiyarsa tun ma kafin ya hau kujerar shugaban ƙasa.

Ana sa ran shugaban zai koma gida a mako na biyu na watan Afrilu, sannan shi ne zai ci gaba da zama a matsayinsa na shugaban ƙasa ba tare da ya mika harkokin mulki ga mataimakinsa ba.

An kama fasto biyu da zargin kisan ƴan sanda a kudancin Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 16 da take zargi da kashe jami'anta a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Wata sanarwa da Frank Mba mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Lahadi, ta ce wasu daga cikin waɗanda aka kama sun amsa laifin kasancewarsu mambobin ƙungiyar IPOB da kuma ESN, waɗanda ke fafutikar kafa ƙasar Biafra.

Frank Mba ya ce an kama wani fasto mai suna Cletus Nwachukwu Egole na Cocin Holy Blessed Trinity Sabbath da wani faston mai suna Michael Uba na ƙungiyar Association of Jewish Faith a Jihar Imo da zargin taimaka wa waɗanda ake zargin.

"Cletus Nwachukwu, wanda aka fi sani da Alewa, da Michael Uba, su ne ke tsara hare-hare kan jami'an tsaro da kuma bai wa gungun mutanen mafaka," a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa: "Ana amfani da gidan Cletus Nwachukwu a matsayin wurin tsara hare-hare sannan ya sadaukar da gonar ɗan uwansa domin amfani da ita wajen bayar da horo da mafaka ga miyagu."